Xi ya yi kira da dunƙule tattalin arzikin Asia da Pasifik yayin da ake fuskantar ƙalubale

Daga CMG HAUSA

Shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin, ya bayyana a yau Alhamis cewa, yayin da ake fuskantar sabbin sauye-sauye, akwai bukatar mambobin ƙungiyar haɗin gwiwar raya tattalin arzikin Asiya da Pasifik wato APEC, su yi waiwaye su dauki darasi daga tarihi, su tunkari ƙalubalen da ake fuskanta yanzu, tare da jajircewa wajen dunkule tattalin arzikin yankin Asia da Pasifik.

Xi Jinping wanda ya bayyana haka cikin rubutaccen jawabin ga taron ƙolin shugabannin masana’antu da kasuwanci na ƙungiyar APEC, ya yi kira da a haɗa hannu wajen samar da sabbin nasarori a fannin ci gaba da gina al’ummar Asia da Pasifik mai makoma ta bai ɗaya.

Ya kuma gabatar da wasu shawarwari 6 game da hakan, waɗanda suka haɗa da, gina tubalin neman ci gaba cikin lumana da ɗaukar dabarun neman ci gaba dake mayar da hankali kan moriyar jama’a da faɗaɗa buɗe ƙofa ga ƙasashen waje da jajircewa wajen hadewa da juna da gina nagartaccen tsarin samar da kayayyaki da kuma ɗaukaka aikin raya tattalin arziki.

A cewar shugaba Xi, yankin Asiya da Pasifik ba wuri ne da kowa zai yi abun da ya ga dama ba, kuma bai kamata ya zamo dandalin takara ga manyan ƙasashe ba.

Yana mai cewa, ba za a amince da duk wani yunƙuri na tayar da wani yakin cacar baka a yankin ba.

Har ila yau, shugaban na ƙasar Sin ya bayyana cewa, bin tafarkin neman ci gaba cikin lumana, muhimmin zabi ne da ƙasarsa ta yi saboda muradun al’ummar Sinawa, kuma za su jajirce ga tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba da haɗin gwiwa da samun moriyar juna.

Haka kuma, za su mayar da hankali ga kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya, yayin da suke neman na su ci gaban, kana za su bayar da ƙarin gudunmuwa ga zaman lafiyar duniya da ci gaba, ta hanyar na su ci gaban.

Da yake bayyana buɗe kofa da dunƙulewa wuri guda a matsayin masu muhimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban bil Adama, Xi Jinping ya ce, ɗaukacin al’ummar Asiya da Pasifik ne suka raya yankin ta hanyar haɗa hannu da shawo kan wahalhalu da ƙalubale.

Yana mai cewa, duk wani yunkuri na kawo tsaiko ko rusa tsarin samar da kayayyaki, da aka samar a yankin cikin shekaru da dama, babu abun da zai haifar face lalata hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin.

Ya ce buɗe ƙofa zai kawo ci gaba, yayin da rufewa za ta haifar da koma-baya.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha