Mbappe na ƙoƙarin maye gurbin Ronaldo a Man United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rahotanni daga lasar Ingila sun bayyana cewa ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester United tana son ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Paris Saint German, Kylian Mbappe a matsayin wanda zai maye gurbin Cristiano Ronaldo.

Kwanan nan ne dai ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya shiga wata tattaunawa mai zafi da Piers Morgan, inda ya nuna ɓacin ransa kan abubuwa da dama na ƙungiyar Man United.

Ronaldo ya ce, baya wani nuna girmamawa ga Erik ten Hag kuma ya yi ikirarin cewa wasu Jami’an ƙungiyar da yawa sun yi yunƙurin tilasta masa ficewa daga kulob ɗin, yayin da kuma ya soki iyalan Glazer.

Ralf Rangnick, Wayne Rooney da Gary Neville suma sune waɗanda Ronaldo ya mayar wa martani, kuma ana sa ran ɗan wasan na Portugal ya buga wasansa na ƙarshe a Man United.

Rahoton ya ƙara da cewa, tun da farko Man United ta shirya ba da fifiko wajen sayen sabon ɗan wasan gaba a bazara mai zuwa, amma za a fara aiwatar da tsare-tsaren sayen ɗan wasan a lokacin hunturu yayin da Ronaldo ke shirin fitar shi daga ƙungiyar.

Man United na iya tsammanin biyan aƙalla fam miliyan 150 don sayen Mbappe, wanda ake zaton za su yi, da kuma fitar da fam 500,000 na albashi na mako-mako ga Bafaranshen.