Magidanci ya daɓa wa surukinsa kwalba

An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, kan zargin daɓa wa surukinsa kwalba a kai.

Lauyan mai gabatar da ƙara, Sufeta Evelyn Motim, ta faɗa wa kotun cewa, mai kare kansa ya aikata laifin ne ranar 30 ga watan Oktoba a yankin Abule Ijaye da ke jihar.

Ta ce, wanda ake zargin ya daɓa wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai.

Ta ce, surukin ya gamu da iftila’in ne bayan da aka gayyato shi don ya zo ya sasanta matsalar aure, daga nan wanda ake zargi ya haɗa baki da wasu suka lakaɗa wa surukin dukan kawo wuƙa.

Lauyar ta ce, wannan laifi ne da ya saɓa wa sassa na 516 da 355 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Ogun na 2006.

Alƙalin kotun ya ba da umarnin a kai wanda ake zargin kurkuku a ajiye zuwa lokacin da zai biya kuɗin beli N50,000 da aka yanka masa da kuma shaida ɗaya.

Daga nan, ya ɗage shari’ar zuwa 23 ga Nuwamba don yanke hukunci.