Me ke kawo tabon fata (3)

Daga AISHA ASAS

Dalilan da ke kawo tabon fata suna da yawa kamar yadda muka sanar tun a baya, don haka ne muka kwashe tsayin lokaci ba mu kawo ƙarshen wannan darasin ba.

Daga cikin su akwai:

Rashin fitar gashi:

Idan aka yi aski, za a ga kalar fatan wurin gashi ta fi ɗan duhu fiye da sauran fatar, wasu na ganin hakan na samuwa ne ta sanadiyyar zaman wurin matsirar gashi, wannan shine bayyanin da za mu iya yi wa kanmu kan wannan duhun.

Sai dai masana sun bayyana cewa, hakan na faruwa ne sanadiyar sinadarin melanin da ke fitowa don ba wa gashin abin da ke haifar masa da baqi a gashin. Duk da cewa an sanar cewa shi sinadarin ba baƙi ba ne wuliq kamar irin na gashi ba, yakan zama baƙin ne a lokacin da ya yi tarayya da abin da ya riska, wannan ne ya sanya yake da bambanci da irin saukar da yake yi a fata.

Ƙarancin wannan sinadari sanadiyyar shekaru ko damuwa, ciwo, yawan jima’i ne ke sa a samu furfura, wadda ta ke farawa daga ƙarancin shi zuwa rashin shi.

A lokacin da gashi ya rasa wannan sinadari, to zai soma fita a halittar shi ta tun asali, wadda shi wannan sinadari ke haɗuwa da ita ya samar da baƙin gashi(mun yi wannan bayyani a darasin da muka yi kan furfura).

Cire gashi da za mu yi ta hanyar aski ba zai hana wannan sinadarin fitowa ba, musamman idan akwai ƙurciya zai fito da yawan sa yadda ya saba, don haka wurin zai ci gaba da samun adadin da aka saba fitarwa, wannan ne zai sa wurin ya yi duhu fiye da sauran fatar jiki.

Yadda za a kawar da wannan baƙin ya samu bambancin ra’ayi na masana, wasu na ganin babu wata hanya halastacciya ta kawar da wannan tabon na matsirar gashi, yayin da suka haramta duk wata dabara da za a yi amfani da ita.

Domin a cewar su, zata iya haifar da yawaitar sinadarin, domin za a iya aika masa da saƙon neman ƙari ba tare da an sani ba, wasu kuma da za a yi amfani da su don rage yawaitan fitowar sa za su iya yin tasiri wanda zai iya kawo illa a gaba, ma’ana lokacin da shekaru suka ja.

Yayin da wasu ke ganin ba wata matsala matuƙar ka yi amfani da irin abin da ya dace, za ka iya rage duhun wurin cikin sauƙi kuma ba tare da barin baya da ƙura ba. A nan zan ce a nemi shawarar masana idan buƙatar hakan ta taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *