Shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Afirka ta Kudu da na ƙasar Senegal

Daga CMG HAUSA

Da yammacin yau Talata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a tsibirin Bali dake ƙasar Indonesia.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin tana raya dangantakar dake tsakaninta da ƙasar Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare, kuma tana son su ƙara imani da juna a fannin siyasa, da sa ƙaimi ga samun ci gaba kan raya dangantakarsu a dukkan fannoni.

Ya ce Sin tana son yin mu’amala da ƙasar Afirka ta Kudu kan fasahohin tafiyar da harkokin siyasa da ƙasa, da goyon bayan Afirka ta Kudu wajen neman hanyar zamanintar da kanta bisa nata salo, da ƙara haɗin gwiwa tsakanin shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” da shirin sake bunƙasa tattalin arziki da farfaɗowa na ƙasar Afirka ta Kudu, da zurfafa haɗin gwiwarsu a fannonin cinikayya da zuba jari, da makamashi da sauransu, da sa ƙaimi ga aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito kansu a gun taron dandalin tattaunawar haɗin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda aka yi a kasar ta Afirka ta Kudu, da goyon bayan kamfanonin Sin don su zuba jari a ƙasar, da kuma faɗaɗa fitar da kayayyakin Afirka ta Kudu zuwa ƙasar Sin.

A nasa ɓangare, shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar abokiya ce ta ƙasar Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare, kuma ƙasarsa za ta ci gaba da goyon bayan ƙa’idar Sin ɗaya tak a duniya.

Kana Afirka ta Kudu tana son koyon fasahohin Sin a fannonin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kyautata tsarin makamashi, da shiga ayyukan raya shawarar “ziri ɗaya da hanya daya”, da kuma ƙara buɗe ƙofa ga kamfanonin Sin don sa ƙaimi gare su, wajen zuba jari da haɗin gwiwa a ƙasar.

Yau da yamma, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Senegal Macky Sall a tsibirin Bali dake ƙasar Indonesia.

Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, bisa ƙoƙarin ɓangarorin biyu, an samu babban ci gaba kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal da kuma Afirka.

Ya ce Sin tana son ci gaba da yin ƙoƙari tare da ƙasar Senegal wajen samun bunƙasuwa da farfaɗowa, da goyon bayan juna kan batutuwan dake shafar cikakken ‘yancinsu, da tsaron ƙasa, da moriyar bunƙasuwa.

Ya ƙara da cewa, Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga ƙasar Senegal wajen gina ayyukan more rayuwa kamar hanyoyin mota, da yankin masana’antu, da kuma fadada fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa ƙasar Sin.

A nasa ɓangare, shugaba Sall ya godewa ƙasar Sin bisa gudummawarta ga Senegal da kuma sauran ƙasashen Afirka, yana mai cewa ta kasance ƙasa ta farko da ta goyi bayan shigar da ƙungiyar AU cikin ƙungiyar G20.

Ya ce ƙasar Senegal ta gamsu da ci gaban da aka samu kan ayyukan da aka cimma daidaito kansu, a gun taron dandalin tattaunawar haɗin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, kana tana son ci gaba da haɗa gwiwa bisa tsarin dandalin tattaunawar.

A wannan rana kuma, shugaba Xi ya gana da firaministan ƙasar Netherland Mark Rutte, da firaministan ƙasar Australia Anthony Albanese, da shugaban ƙasar Argentina Alberto Fernández, da firaministan ƙasar Spaniya Pedro Sánchez, da kuma shugaban ƙasar Koriya ta Kudu Yoon Seok-Youl.

Mai fassara: Zainab