Ma’auratan zamani da zama a gidan gandun

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku na zamantakewa a jaridarmu mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan makon muna tafe ne da magana a game da zaman ma’aurata a gidan gandu. A sha karatu lafiya.

Ma’anar gidan gandu

Bahaushe tun fil’azal yana da al’adar zaman gandu. Zaman gandu ba wani abu ba ne illa, zama irin na zamanin da, wanda Maigida zai shaci fili ya gina gidansa ya katange sauran. Kwanci tashi, idan yaransa maza sun fara tashawa, sai ya yi musu aure.

Kuma kowanne idan aka yi masa auren, za a yankar masa wani ɓangare na wannan gidan gadon a ba shi ya je ya zauna da matarsa. Da ma kuma tun bayan cikar sa shekaru 7 a Duniya, bayan an yi masa kaciya, akwai gona ta gado, makekiya.

Ita wannan gonar a ciki ake yanke masa abinda ake kira da ‘gayauna’ sai ya fara koyon nomansa da kansa. Tun yana gwadawa kamar wasa, har ya zo ya ƙware. To daga ya isa aure, an yi masa ɗaki, an yi masa aure (don galibi iyaye ke sa kuɗin su yi wa yaro aure, a wancan lokaci), sai iyaye su cigaba da ɗaukar ɗawainiyar wannan matar tasa da ciyar da ita da duk ma wani abu da ya rataya a wuyan miji.

Idan ta haihu ma, hidimar suna da haihuwa, duk iyayen miji suke yi. Sannan raino da yaye yaro da sauran abubuwa duk iyayen suke yi. Ba su yarda yaro ya je ya yi gidansa can nesa ba sun san ba zai iya ɗawainiya da matar ba.

A gidan gandu, shi Maigida/Uba shi ne, shugaba mai cikakken iko a gidansa. Yadda ya ce haka za a yi. Kuma idan ya sa doka, ko a kan ‘ya’yansa, ko matansa, matan ‘ya’yansa har jikoki dole ba wanda ya isa ya ƙetara. A wancan zamani akwai wata kunya ta musamman tsakanin suruki da iyayen miji.

Ana matuƙar kunya da girmama juna. Dai-dai da unguwa, wasu matan ma sai dai su tambayi Maigida ba mazajensu na aure ba. Kuma kada mu manta, dukkan yaransa maza a cikin gidan gandun suke zama a yankar musu waje a yi musu ɗaki su zauna da iyalansu.

Haka su ma idan nasu yaran sun taso, a cikin gidan dai za a yankar musu. Haka za a ga gida ya tumbatsa ya cika tinjim! Sannan kuma duk da yawansu, tukunya guda ake ɗorawa ta girkin gidan. Kuma sabuwar amarya sai ta yi haihuwa biyu ko uku ma ba ta fara girki ba. Sai dai a dafa a ba ta, Bama takan taya su da aikin gida.

Alfanun zaman gandu ga ma’auratan

*Amfani na farko shi ne, tunda ma’auratan yara ne, suna buƙatar jagorancin manya koyaushe da sa musu ido don kada wata da yarinta ta sa su yi kura-kurai a zaman aure.

*Mace takan koyi aikin gida, kamar girki da raino dukkan a wajen iyayen mijinta.

*Mace ba ruwanta da girki sai ta kai wasu shekaru masu yawa.

*Taimaka wa amarya kada kaɗaici ya dame ta. Samun mutane a gidan da dama zai cire mata kaɗaici da kewa.

*Miji ba ruwansa da cefane. Da mai shi, da mara shi dukkan za a dafa a ba su tare da iyalansu.

*Taimaka wa mace da raino, da sauran abubuwan gida.

*Idan matsala ta faru tsakanin ma’aurata, iyayen miji kan shiga su sasanta. Shi ya sa da wuya a samu rabuwar aure a wancan lokacin.

*Akwai girmamawa a tsakanin suruki. Ita matar na gani su a iyaye, su ma surukan suna ganinta, a ‘ya.

*Akwai taimakeniya tsakanin faccaloli (matan wa da ƙarni ko ƙanne).

*Idan wata matsala ta faru, kamar goyon ciki ko naƙuda, akwai dattijai da za su kawo ɗauki ko da mijin ba ya gida, ko idan mai tafiye-tafiye ne.

Waɗannan kaɗan daga cikin amfanin dake akwai na al’adar Bahaushe ta zaman gidan Gandu.

Zaman gandu a wannan zamanin

Duk da kasancewa al’adar zaman gandu tsohuwar al’ada ce, amma har yanzu musamman a ƙauyukan ko a wuraren da ba su da ƙarfi sukan aiwatar da ita. Wani zubin ma ba wai zama da iyayen ba ne, har ma ‘yanuwa sukan yi gida, ko iyaye su ba su gida guda su zauna da matansu kowa da ɗakinta ko ɓangarenta daban. Sai dai kuma zaman na yanzu ba ya ƙarko kamar na da. Mai yiwuwa saboda canzawar rayuwa da kuma surukuta irin ta zamani. Shi ya sa abin ba ya daci kamar na da.

Matsalolin zaman gidan gandu a wannan zamani

*Da farko dai, surukai na yanzu ba lallai su yi biyayya irin ta wancan zamani su sakar wa iyayen miji wuƙa da nama ba. Dalili kuwa, waɗancan ƙananan yara ake aurowa, babu wannan wayewar da bijirewar. Amma yanzu an auri mace tar take ganin kowa. Wata ta shekar 20, 23, 25, wasu ma har 30 a gaban iyaye, wanne iko iyayen miji za su nuna musu?

Ai ko abincin da ake yi na gabaɗaya, in dai ba mijin ne ba shi da ƙarfi ba, da wuya a ce sun yarda an haɗa girki da iyayen miji. Wasu lokutan ma, shi kansa ɗan na yanzu wani ba girmama iyayen nasa yake ba, balle matar ita ma ta gani ta koya. Yadda ya raina uwarsa ita ma haka za ta raina ta.

Wannan shi yake kawo rigimar. Sai uwar miji ta dinga shiga abinda ba ruwanta, ita kuma surukan sai ta raina ta. Sai ka ga ana sa toka, sa katsi. Sannan su ma dangin mijin kullum suna gidan, sun zo wajen uwarsa. Haka wannan miji su ma za su iya yi mata rashin kunya suna ganin ai cin arzikin yayansu ta zo yi.

*Gulmace-gulmace: Zaman taren yana ba da damar gulma. Ƙanne miji da suke gidan suna shige da fice a ɗakin matar ɗan uwansu sai su dinga ɗaukar zance, wani zubin har da ƙarya, suna gaya wa uwarsa, wannan yana haɗa faɗa sosai.

*Abu na uku, a lokacin da sababbin ma’aurata suka yi aure, dole suna buƙatar wani ɗan lokaci za su fuskanci juna. Kuma za a dinga samun ɗan saɓani kafin fahimtar juna ta tabbata. Idan ya kasance ba su kaɗai ba ne, to akwai wahalar a samu wannan fahimtar. Domin zuga da baki za su yi tasiri sosai.

*Sannan akwai matsalar zaman mata waje guda akwai matsala. Domin akwai gutsiri-tsoma.

*Idan faccakoli ne kuma, akwai gasa. Gasar ita ke kawo gulma da faɗa a tsakaninsu. Idan aka samu ɓaraka kuma, sai mazuga daga dangin miji ko daga waje su samu abin yi. Za su yi ta iza wutar. Shi ya sa da wuya faɗan ya ƙare.

*Sannan raini na samun mazauni a tsakanin mace da iyaye da dangin miji. Saboda zaman waje guda. Ido aka ce wa ka raina, wanda nake gani kullum!
A ɓangaren matar kuma

Mace ma tana da matsalolin zaman gandu kamar haka

*Gurvacewar tarbiyyar yara. Idan mace na zaune a babban gida kamar na Gandu, sai ta sha wuya kafin ta samu ta riƙe ragamar tarbiyyar yaranta. Sai abin ya zama kamar tana tufka wasu yaran da iyayensu suka gaza musu tarbiyya suna warware wa.

*A ɓangaren matar ba ta da wani sirri saboda gida ne na gani-ga ka. Babu wata sakewa.

Duba da waɗannan matsaloli da ma wasu, shi ya sa a halin yanzu maza da yawa suke gudun zaman gidan gandun. Haka ma mata da yawa da za a ba su zaɓi ba za su yarda su zauna a gidan gandun ba saboda matsalolinsa. Wannan ya kashe wa zaman gandun kasuwa. Gidaje dai yanzu a birni ba a ƙauye ba da wahala a samu wannan.

A nan za mu tsaya, sai mako mai zuwa, idan rai ya kai.