Kyautata alaƙar Sin da Amurka na iya shawo kan matsalolin duniya

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Yayin da taron ƙoli na ƙungiyar G20 zai mayar da hankali wajen tattauna muhimman batutuwan da ke ciwa duniya tuwo a kwarya, kamar na tattalin arziki da wadatar abinci da makamashi da batun Ukraine da sauransu, ya samar da wata muhimmiyar dama ta tattaunawar keke da keke, tsakanin shugabannin manyan ƙasashen duniya biyu, wato Sin da Amurka.

Karon farko tun bayan hawansa karagar mulkin Amurka, shugaba Joe Biden ya gana ido da ido da takwaransa na ƙasar Sin Xi Jinping a jiya, gabanin taron.

Haƙiƙa, wannan wata dama ce ta warware zare da abawa game da batutuwan dake haifar da tsamin dangantaka tsakanin manyan ƙasashen biyu.

Amurka ta daɗe tana takalar ƙasar Sin da gangan, yayin da a kullum, ƙasar Sin kan gargadi Amurkar tare da jan hankalinta game da muhimmancin girmama juna da haɗin gwiwa a tsakaninsu.

Da alama za a samu sauƙin abubuwa, duba da yadda shugaban na Amurka ya nanata cewa, matsayar ƙasarsa ta kiyaye manufar Sin ɗaya tak a duniya ba ta sauya ba, kuma ba ta son gogayya tsakaninsu ta rikiɗe zuwa rikici.

Gogayya ko Takara mai tsafta tsakanin manyan ƙasashen biyu mai, za ta iya zama mai amfanawa al’ummunsu da kuma duniya, muddun Amurka ba ta ci gaba da yin amai tana lashewa ba.

Kamata ya yi ta ɗauki shawarar ƙasar Sin, wato mutunta juna da girma cikakken ’yanci da moriyar juna, su kasance tushen hulɗar ƙasashen biyu.

Kana akwai buƙatar ’yan siyasar Amurka, su fahimta tare da kiyaye furucin na shugabansu, su dakatar da duk wani yunƙurin lalata dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu da neman haddasa rigima.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, a matsayinsu na shugabannin manyan ƙasashe biyu, ya kamata su lalubo hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu, domin yanayin da take ciki a yanzu, ba ta dace da moriyarsu da ma ta ɗaukacin al’ummar duniya ba.

Ba shakka, ƙasashen duniya na mayar da hankalinsu ga irin yanayin da Sin da Amurka ke ciki.

Kyautata alaƙa a tsakaninsu za ta iya magance sama da rabin batutuwan da duniya ke fuskanta.

Haka kuma, za ta kasance abun koyi ga ƙasashe masu tasowa.

Ya kamata Amurka ta mara baya ga yunƙurin Sin na tallafawa ƙasashe masu rauni da ma waɗanda ke tasowa, maimakon ta rika yi mata zagon ƙasa ko neman bata mata suna.

Sin ta yi an gani, kuma tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya duk da tarin nauyin al’umma biliyan 1.4 dake wuyanta a cikin gida.

Idan har da gaske Amurka na son kyautata dangantakarsu domin duniya baki ɗaya ta amfana, ya kamata ta dakatar da rajinta na bata sunan ƙasar Sin da yada ƙarairayi, ta rungumi hanyar zaman lafiya da bayar da gudunmawa ga ƙoƙarin Sin domin kai wa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga ɗaukacin bil adama.