Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mahukunta a Abuja Babban Birnin Tarayya ta fatattaki mabarata da ke galantoyi a sassa daban-daban har 273 sannan sun kama ababen hawa 670 domin daƙile muggan ayyuka a Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja Wale Ajao ya sanar da haka ranar Talata a taron da ya yi da manema labarai kan matsalolin rashin tsaro da aka yi a gidan Ministan Abuja Nyesom Wike.
Ajao ya ce mabaratan na tsare a ofishin Kula da inganta al’umma domin kulawa da su zuwa lokacin da za a maida su garuruwansu.
Mahukuntan sun ce za a ci gaba domin ganin sun fatattaki masu gararramba da a faɗin Abuja.
Ya ce gwamnati ta kama ababen hawa 670 dalilin karya dokar amfani da hanya, rashin takardun da ya kamata na ababen hawa, amfani da gilasai masu duhu ba tare da izinin ba, rashin lambar lasisi da yin amfani da ababen hawan a wuraren da bai kamata ba.
Ajao ya ce mahukuntan sun kama wasu mutane bisa ga laifin safarar muggan ƙwayoyi kuma ta damƙa su hannun Hukumar NDLEA.
Idan ba a manta ba Wike ne ya ƙaddamar da ‘Operation Sweep’ domin kawar da mabarata, masu satar mutane, gungun ‘yan fashi da makami, da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka. ƙudurin yana da nufin maido da aminci kiyaye doka da mutuncin garin.
Wannan matakin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke a watan da ya gabata na korar ƙarar da ke neman hana ministar koran mabarata a garin.
Ajao ya ce mataki na gaba zai ƙunshi tsaurara dokokin amfani da hanya, amfani da baƙin gilasai a mota ba tare da izinin ba da hukunta duk waɗanda ba su yi wa motocin su rajista da samun lambar mota da ya kamata ba.
Wike ya bada umarnin hana haƙo ma’adanai musamman ba tare da izini ba sannan ya bada umarnin tada duk sansanin ‘yan gudun hijira da aka kafa ba bisa doka ba.
