Daga USMAN KAROFI
Dakta Hakeem Baba-Ahmed, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan siyasa, ya yi murabus daga muƙaminsa. Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa tsohon mai magana da yawun ƙungiyar dattawan Arewa (NEF) ya miƙa takardar murabus ɗinsa kusan makonni biyu da suka gabata. Sai dai, bai bayyana takamaiman dalilansa ba, illa dai ya ce murabus ɗin nasa ya biyo bayan wasu dalilai na sirri. Har yanzu ba a tabbatar da ko fadar shugaban ƙasa ta amince da murabus ɗin nasa ba.
Baba-Ahmed, wanda aka naɗa a watan Satumba 2023, ya taka rawa a siyasar Najeriya, musamman wajen kare muradun Arewa. A lokacin da yake riƙe da muƙamin, an samu saɓani tsakaninsa da ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, wanda ya soki dangantakarsa da NEF. Matawalle ya yi kira ga ‘yan Arewa masu muƙami a gwamnatin Tinubu da su fito fili su kare manufofin gwamnati, amma Baba-Ahmed ya mayar da martani yana mai cewa ya fi dacewa a bayyana irin gudunmawar da ministocin Arewa ke bayarwa maimakon sukar NEF.
Dr. Baba-Ahmed ya shafe shekaru da dama a aikin gwamnati, inda ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da babban sakataren ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da kuma sakataren hukumar zaɓe ta INEC. Yana da digirin digirgir (PhD) daga Jami’ar Sussex, kuma ya taɓa zama malami a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Kafin naɗa shi a matsayin mai ba da shawara kan siyasa, ya jagoranci sashen yaɗa labarai na NEF, inda ya yi fice wajen kare ra’ayoyin Arewa kan al’amuran ƙasa. Murabus ɗinsa na ƙara haifar da ce-ce-ku-ce kan tasirinsa a cikin gwamnatin Tinubu.
