
Daga BELLO A. BABAJI
A yayin da masu sauraro suka kunna gidan rediyon VOA a makon da ya gabata, sun jiyo waƙoƙi suna tashi a madadin shirye-shirye, wanda hakan alamu ne da ke nuna cewa sojoji da gwamnati sun karɓe iko da gidan.
A ranar Juma’a ne aka dakatar da gidan rediyon, wanda ƙasar Amurka ke ɗaukar nauyin yaɗa shirye-shiryensa.
An dai fara sauraron shirye-shiryensa na Hausa ne a yankin Yammacin Afirka tun a shekarar 1979.
Lamarin da ya haifar da tsaiko acikin al’ummar Arewacin Nijeriya musamman Hausawa da ke yawan sauraren labarai da wasu shirye-shirye a gidan rediyon.
Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta dakatar da tashar daga gudanarwa a ƙasashen Afirka musamman wanda mazauna ƙauyuka a Nijeriya, Nijar, Kamaru, Ghana da makamantansu ke sauraren sa.
Al’umma da dama sun amince da VOA a matsayin fagen samun sahihan labarai da kuma nuna ƙwarewa a harkar jarida.
Ana zargin tun a zangon farko na mulkin Shugaba Trump, ya yi yunƙurin siyasantar da tashar, inda a yanzu da ya ke wa’adi na biyu, ya rushe batun ɗaukar nauyin ta da gwamnatin ƙasar ke yi.
