
Daga BELLO A. BABAJI
Alƙali Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta haramta wa waɗanda aka zayyano sunayensu a ƙarar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar akan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da wasu ɓangarori uku yin hira da manema labarai akan al’amuran da suka shafi dakatarwar da aka yi wa Natasha na watanni shida.
Nyako ta yi hukuncin ne bayan wani ƙorafi da Lauyan Akpabio, Kehinde Ogunwumiju (SAN) ya yi akan Natasha, kan cewa ta na yin hira akan batun ƙararta da ke kotun wanda ba a kammala hukunci a kai ba.
A yayin hukuncinta ne, Alƙali Nyako ta yanke cewa, babu wata hira da aka amince wa ɓangarori biyun ko lauyoyinsu su yi akan matsalar.
Haka kuma, ta haramta masu tattauna matakin da ƙarar ke ciki game da shari’ar a Soshiyal Mediya.
Lauya Ogunwumiju ya ce, Natasha ta na zuwa gare gidajen jaridu ta na tattauna batun rikicin da ke tsakanin ta da Akpabio, inda ya ce daga cikin su akwai BBC da CNN.
Daga bisani Alƙalin ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Mayu, inda ta ce sai an gabatar sauran rahotanni daga majalisar dattawan da ke da alaƙa da batun dakatar da ita daga majalisar, wanda a kai ta shigar da ƙarar, kafin a yi hukunci.
