Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dr Idris AbdulAziz

Spread the love

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar malamin addinin musuluncin nan mazaunin Jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz, wanda ya rasu da sanyin safiyar Juma’a yana da shekaru 68.

Wata sanarwa da ta fito mai ɗauke da sanya hannun mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan dabarun yaɗa labarai ta ce, Shugaban ya bayyana malamin a matsayin wanda ke da jimirin tsayawa akan gaskiyarsa kuma wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen gyaran tarbiyar miliyoyin matasa da sauran al’umma kan hanyoyin inganta aƙida.

Shugaban ya kuma yaba da irin gudunmawar da Dr Abdulaziz ya bayar wajen daƙile yaɗuwar ta’addanci musamman a farkon rikicin Boko Haram inda ya jaddada cewa za a yi kewar kiraye-kirayen da malamin kan yi da babbar murya kan a yi gyara da nuna sanin yakamata.

Shugaba Tinubu ya rufe da addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, ya kuma bai wa iyalansa da mabiyansa damar yin koyi da ayyukansa na alheri.

By ukarofi