NNPCL: Ojulari ya amshi ragamar aiki daga hannun Kyari

Spread the love

Sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Bayo Ojulari, ya karɓi ragamar jagorancin kamfanin daga hannun tsohon shugaba Mele Kyari a wani bikin miƙa mulki da aka gudanar a shelkwatar kamfanin a ranar Juma’a. Ojulari ya yabawa Kyari bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban kamfanin da kuma hidimar da ya yi wa ƙasa. Ya bayyana cewa zai yi ƙoƙari wajen ci gaba da nasarorin da aka samu, tare da ƙarfafa kamfanin domin cimma sabbin burikan da aka gindaya.

A yayin jawabinsa, Ojulari ya bayyana cewa babban burinsa shi ne haɗa kai da ma’aikatan kamfanin don tabbatar da nasarar shirin shugabancinsa. Ya kuma jaddada cewa zai nemi shawarar Kyari lokaci-lokaci domin samun nasarar jagorancin kamfanin. A nasa bangaren, Kyari ya taya Ojulari murna da fatan alheri, tare da alƙawarin bayar da goyon baya a duk lokacin da ake buƙata.

Bugu da ƙari, NNPCL ta sanar da naɗin sabbin manyan jami’ai guda takwas da za su yi aiki tare da Ojulari. Cikin su akwai Rowland Ewubare a matsayin babban jami’in ayyuka, Adedapo Segun a matsayin babban jami’in Kudi, da Olalekan Ogunleye a matsayin mataimakin shugaba kan harkokin iskar gas, lantarki da sabbin makamashi. Sauran sun hada da Udy Ntia, Mumuni Dangazau, Sophia Mbakwe, da Adesua Dozie, waɗanda za su taka rawa wajen tafiyar da sabon shugabancin kamfanin.

By ukarofi