Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla mutum 10 ne wasu mahara suka kashe a daren ranar Laraba a ƙauyukan da suka kai hari a ƙaramar Hukumar Bokkos da ke jihar Filato.
Shugaban Hukumar Raya Al’adun Gargajiya ta Bokkos (BCDC) na Jihar, Farmasum Fuddang, da sakatare, Ambasada Duwam Bosco, ne suka bayyana hakan a wata sanarwar haɗin gwiwa da suka sanya wa hannu a ranar Alhamis.
“A cikin mako ɗaya kacal, mun yi asarar ‘yan uwa sama da 20 sakamakon waɗannan ‘yan ta’adda da ke ci gaba da kai harin ƙabilanci da addini a ƙauyuka biyar. A ranar 2 ga Afrilu kaɗai, sun kashe sama da mutane 10,” inji BCDC.
ƙungiyar ta kuma ƙara da cewa, maharan sun ƙaddamar da harin ba-zata da rana a garin Mangor Tamiso sannan suka koma Daffo da Manguna inda suka mamaye ƙauyukan Hurti da Tadai.
“Dukkan godiya ga sojoji da ‘yan sandan Nijeriya saboda saurin amsa kiran gaggawa da suka yi, wanda ya taimaka wajen rage asarar rayuka,” inji sanarwar.
ƙungiyar ta ƙara da cewa, idan aka yi la’akari da ƙalubalen kayan aiki da ma’aikata da cibiyoyin ke fuskanta, an yi kira ga ɗaukacin ‘yan asalin Bokkos da su yi biyayya ga shawarar Gwamna Caleb Mutfwang na kare kansu.
