Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗora haraji na 0.5% kan dukkan kayan da za a shigo da su ƙasashensuu daga ƙasashe da suke mambobin ƙungiyar raya tattalin arziƙi na yammacin Afirka (ECOWAS).
A cikin wata sanarwa ta haɗin guiwa a makon da ya gabata, ƙungiyar AES ta ce tana son amfani da wannan dama ce wajen tafi da ayyukan ƙungiyar.
Harajin wanda ya fara aiki daga ranar Juma’ar da ta gabata zai shafi duk wani kaya da za a shigo da su ne daga ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS da za su shiga cikin ƙasashen uku.
Wannan sabuwar doka dai ta ci karo da yunƙurin da ƙungiyar ECOWAS ke yi na bai wa ƙasashen da ke ƙungiyarta da har ma da na AES damar shigar da kaya ba tare da shinge ba duk kuwa da ficewar ƙasashen uku daga ƙungiyar a watan Janairu.
ECOWAS ta tabbatar da cigaba da bai wa kayan da ake shigo da su daga ƙasashen uku damar wucewa ba tare da shinge ba kamar yadda tsarin cinikayya da zuba jari na ƙungiyar (ETLS) ya tanada.
Tsarin ETLS ya shafi kasuwanci ba tare da ɗora haraji ba kan kayayyaki da ayyukan hidima a tsakanin ƙasashen da ke ƙungiyar ta ECOWAS.
Sai dai ta hanyar ɗora wa dukkan kayan da suka fito daga ECOWAS, hakan na nufin AES za ta haifar wa da tsarin kasuwanci na ETLS tarnaƙi.
Sabuwar dokar dai na iya ƙarin abin da ake kashewa wajen cinikayya da musayar kayayyaki da haifar da tsadar kayayyaki a ƙasashen AES wanda kawo harkar shigo da kaya tarnaƙi da gurgunta manufar ECOWAS na kasuwanci ba tare da shinge ba.
A farkon shekarar 2024 ne ƙasashen Niger da Mali da Burkina Faso suka sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar ECOWAS bayan shafe watanni suna musayar yawu da ƙungiyar.
Shugabannin sojin ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da gaza yaƙi da ayyukan ta’addanci da ƙaƙaba wa ƙasashen takunkumin da ya cutar da mutanensu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen uku.
Sannan ƙasashen sun yi watsi da tayin da ECOWAS ta yi musu na sake duba matakin da suke shirin ɗauka na ficewa daga cikinta.
Sai dai bayan ficewarsu, ECOWAS ta sake jaddada wasu damarmaki ga ƙasashen uku.
Damarmakin sun haɗa da cigaba da ƙin karɓar harajin kayayyaki da ba su damar shiga kowacce ƙasa da ke ƙarƙashin ƙungiyar ba tare da biza ba da damar iya zama a ƙasashen.
Haka kuma ECOWAS ta ayyana “barin ƙofarta a buɗe” ga ƙasashen idan suna so su dawo cikinta. Sai dai wannan sabon haraji da suka ƙaƙaba da yuwuwar ya ƙara sa dangantakar ƙasashen da ƙungiyar ECOWAS ta ƙara tsami.
Haka zalika, Nijar ta fice daga ƙungiyar yaƙi da ta’addanci ta yakin yammancin nahiyar Afirka wacce ta ƙunshi sojoji daga Nijeriya da Chafi da Kamaru waɗanda a baya suke aiki tare tun 2015 wajen yaƙi da ta’addanci.
A shekarar da ta gabata ce, ƙasar Chadi ta yi barazanar ficewa daga haɗakar sojin bayan da aka kashe kusan sojoji a 40 a barikinsu.
Sai dai ita Nijar tuni ta ɗauki wannan mataki bayan wata sanarwa a ranar Lahadi ta gidana talabijin na ƙasar, inda a hukumance ta sanar da ficewar tata.
Wannan sabon tsari akwai yuwuwar ya shafi yunƙurin samar da tsaro da ake yi a yankin tafkin Chadi. Yankin dai ya sha fama da ayyukan ‘yan ta’adda ciki kuwa har da ayyukan ƙungiyar Boko Haram.
