Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai ba wa Shugaban ƙasa shawara ta musamman kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya taya al’ummar musulmin Nijeriya barka da sallah bayan kammala ibadar azumin watan Ramadana.
Ribadu, a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, ya buƙaci haɗin kai a tsakanin ‘yan Nijeriya domin cigaba da samun nasarar murƙushe matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Ya ce, wata mai alfarma na Ramadana yana koya mana juriya da tsantseni da sadaukarwa a yayin da ya buƙaci al’umma su yi riƙo da waɗannan kyawawan ɗabi’u wajen haɗa kai domin inganta tsaro.
“Haɗin kanku a ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci da sauran nau’o’i na barazana da ake fama da su muhimmin abu ne wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar nan, musamman ma a salo na gwamnatinmu na shugo da kowa domin ba da gudunmowa.”
“Don haka, ya buƙaci a cigaba da samun haɗin kai tsakanin gwamnati da malaman addinai da al’umma da jami’an tsaro domin yaƙi da ta’addanci da kuma tsattsauran ra’ayi – hakan na da matuƙar muhimmanci.”
“Bukin sallah ƙarama, wani lokaci ne zurfafa tunani da yin godiya da sabunta fatanmu wajen himmatuwa ga samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.”
“Kenan, muhimmin abu ne yadda ‘yan Nijeriya za su haɗu guri guda tare da riƙo da ƙaunar juna wanda ke da muhimmanci ga cigaban ƙasar nan.”
Ribadu ya ce zaman lafiya da haɗin kai da tausasawa su ne muhimman abin da ake nema a lokacin bukin sallah.
Sannan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su cigaba da nuna tausayin juna da kyautatawa da iya zama da juna a yayin wannan buki na sallah da bayansa.
Haka zalika, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su zamo masu kula da duk wani abu da zai zama barazana ga zaman lafiya da nufin samar da al’umma da ke da haɗin kai da yalwar arziƙi ba tare da la’akari da bambancin addini.
“Gwamnatin shugaba Tinubu da ofishina mun himmatu ne wajen tabbatar da tsaron dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da inda suka fito ko addininsu ba.”
“Za mu cigaba da mai da hankali da jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci da mummunan tsattsauran ra’ayi a lokaci guda kuma mu cigaba ɗabbaƙa kira na zama da juna lafiya da tsaro.”
“Ina yi muku barka da sallah,” Ribado ya faɗa.
