Daga DAUDA USMAN a Legas
Wani babban manomi a ƙaramar Hukumar ɗandume dake cikin jihar Katsina mai suna Alhaji Amiru Ɗahiru Ɗanliman ya koka bisa ga matsalolin da harkokin noma ke fuskanta a ƙaramar Hukumar Ɗandume da ma Jihar katsina bakiɗaya.
Babban manomin ya cigaba da bayyana wa Jaridar Blueprint Manhaja a Ɗandume cewar haƙiƙa daga ‘yan shekaru kaɗan baya da suka gabata zuwa wannan shekarar ta bana harkokin noma da masu yin noman da sauran ‘yan kasuwa a ƙaramar hukumar ɗandume sun shiga wani hali na matsaloli masu yawa, inda ya ce kaɗan daga cikin matsalolin kuwa sune idan manomi ne kai ko ɗan kasuwa duk inda kake ko gona ko kuma kasuwa hankalinka ba kwance yake ba saboda tsoron haɗuwa da ‘yan bindiga ko kuma masu garkuwa da mutane a hanyarka ta dawowa gidanka, ya ce haka kuma idan hakan ba ta kasance ba suna iya biyoka gidanka cikin dare su yi maka abinda suka ga dama su fita su yi tafiyarsu.
Ya ce akan haka yake ganin ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane matsalolin manoman jihar Katsina.
Ya yi addu’ar fatan Allah Ubangiji ya kawo wa al’ummar ƙaramar Hukumar ɗandume ɗauki tare da sauran ƙananan hukumomin da harkokin ta’addanci suka yi ƙarfi a jihar Katsina, ya ce ya san irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ta Katsina take yi a wajen ɗaukar matakan da suka dace domin shawo kan al’amarin ya ce a kan haka al’ummar karamar hukumar ɗandume dama na jihar Katsina bakiɗaya suke miƙa saƙon godiyarsu ga mai girma Gwamnan jihar Katsina Dakta Alhaji Dikko Umar Raɗɗa dangane da wannan irin namijin ƙoƙarin da yake yi wa talakawansa a Jihar Katsina a wajen kare lafiyarsu da dukiyoyinsu gabaɗaya.
Hakazalika ya cigaba da roƙon gwamnatin jihar ta Katsina da ta daure ta kyale manoma masu noma filayenta na yankin Birningwari su cigaba da noma kamar yadda suka saba nomawa domin a cewarsa fili ne da ɗumbin al’umma suke nomawa suna cin abinci saboda haka yake ganin ya kamata gwamnati ta kyale manoman kada ta tashe su domin kada wurin ya zama sansanin ‘yan ta’addan dajin Birningwari a cewarsa da fatan Allah Ubangiji ya ƙara taimakon Gwamnatin Jihar Katsina bisa ga ƙoƙarin da take yi wa talakawa da sauran al’ummar jihar baki ɗaya.
Haka kuma ya cigaba da isar da wani roƙon ga gwamnatin jihar cewa ya sani duk shekara tana bai wa ƙananun manoma takin zamani domin ƙara bunƙasa harkokin noma amma manyan manoma ba su samun irin wannan tallafi, ya ce akan haka yake roƙon gwamnatin jihar ta Katsina da ta sanya manyan manoma jihar a cikin wannan tsarin domin suma manyan manoman su cigaba da samun irin wannan tallafi.
A ƙarshe ya ce yana yi wa mai girma gwamnan jihar Katsina barka da Salla tare da sauran al’ummar jihar gabaɗaya.
