Mai wushirya ya fasa auren ‘Yarguda

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Fitaccen ɗan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya
bayyana cewa ba zai auri Basira ’Yar Guda da kotu ta umarce shi bayan tuhumarsa da wasu laifukan watsa baɗala a kafafen sada zumunta.

Cikin wani sabon bidiyo da Mai Wushirya ya fitar, a yau ranar Alhamis ya bayyana cewa duba da ƙorafe-ƙorafen da iyayensa suka yi da sauran abokansa, yana shaida wa mutane cewa idan ya tashi aure zai sanar da su.

Ya ƙara da cewa da ma ba a son ransa ya amsa cewa zai auri ƴar Guda ba, tsoro ne na hukuncin kotu.

Sannan Mai wushirya ya ce yana kira da duk waɗanda suka karɓi kuɗin gudunmawa da sunan wannan biki da su kai kuɗin ga mabuƙata da marayu.

Idan za’a iya tunawa a ranar Talata da ta gabata ne dai kotun Majistiri ta umarci hukumar Hisba ta Jihar Kano da ta ta ɗaura aure tsakanin Ƴan Tiktok din nan guda biyu, Ashiru Mai Wushirya da ‘Yar Guda.

Hukumar tace za a sanya mai wushirya cikin auren gata da hukumar Hisba ta ke yi, mataimakin babban kwamandan hukumar na Kano, Dakta Mujaheed ya bayyana ga manema labarai, a Kano

A cewar Mujahideen Aminudeen hukuncin ya yi daidai duba da yadda hukumar ta Hisbah ke yaƙi da aikata baɗala da abubuwan da suka saɓawa al’ada da addini.

Sannan Malamin ya ce za a sanya su cikin shirin auren gata da hukumar za ta aiwatar bisa sahalewar gwamnatin jihar.

To sai dai kuma, ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) ta bayyana cewa kotu ba ta da ikon tilasta wa Mai wushirya auren Ƴarguda

NBA ta nuna rashin amincewarta da rahotannin da ke cewa wata kotun majistare a Kano ta umarci wasu fitattun masu amfani da TikTok, Idris Mai Wushirya da Basira Yarguda, da su yi aure cikin kwanaki 60, bayan tuhumar da ta shafi wallafa wani bidiyo da ake ganin bai dace ba.

Ƙungiyar ta buƙaci a sake duba wannan hukunci da alƙaliyar kotun, Halima Wali, ta bayar, tare da kiran hukumomin shari’a da su ɗauki matakai domin hana irin wannan umarni mara tushe nan gaba.

Kazalika, ta umarci Kwamitin kare ‘yancin jama’a da kwamitin mata na NBA da su sa ido a lamarin domin tabbatar da cewa doka ta yi tasiri yadda ya kamata.

By ukarofi