Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sallami jagororin tsaro, ya naɗa Janar Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauye-sauye a muƙaman rundunar soji ciki har da tsige Janar Christopher Musa Gwabin a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) da maye gurbinsa da Janar Olufemi Oluyede.

Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana haka a wata takarda, yau Juma’a.

A cewar saƙon, sauye-sauyen za su fara aiki ne a nan take, waɗanda ɓangarori ne na inganta harkokin tsaro a Nijeriya duba da sababbin barazanar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Janar Oluyede shi ne shugaban sojojin ƙasa gabanin ya zama babban hafsan.

Ya kuma karɓi kujerar ne daga Janar Musa, wanda aka naɗa tun a watan Yunin 2023, sannan ya kula da lamuran atisayen daƙile ayyukan ta’addanci da wasu ƙalubalen tsaro a faɗin Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauyin zai fara aiki ne a nan take.

Sauran jagororin da aka naɗa a wasu muƙamai sun haɗa Shugaban sojoji, wato Manjo Janar W. Shaibu; Shugaban sojojin sama AVM Aneke; RA I. Abbas wanda shi je sabon shugaban sojojin ruwa. Haka kuma akwai shugaban sashen Leƙen Asiri na hedikwatar tsaro Manjo Janar E.A.P Undiendeye, wanda ya cigaba da zama a muƙaminsa.

By Babaji