Maimakon maimaita buƙatar “samarwa kai kariya” kamata ya yi Amurka ta nazarci ainihin dalilin kafa hulɗar diflomasiyya tsakanin ta da Sin

Daga CMG HAUSA

Tun lokacin da gwamnatin Amurka mai ci ta kama aiki, jami’an ta ke ta maimaita batun bukatar “samarwa kai kariya”, ƙarƙashin dangantakar dake akwai tsakanin Sin da Amurka, to amma kuma har kawo yanzu, Amurka ba ta fayyace ainihin abun da take nufi da samarwa kai kariya ba.

Yayin taron manistocin ƙasashen wajen sassan 2 a jiya Asabar, wanda ya gudana a birnin Bali, an tabbatar da wanzuwar ƙarya da sassan biyu ke da ita ƙarƙashin dangantakar su cikin tsawon lokaci, don haka abun da ake buƙata yanzu, shi ne ɓangaren Amurka ya karfafa wannan moriya, tare da tsayawa kan magana guda, da aiwatar da matakai ba tare da kaucewa ba.

Ganawar manyan jami’an na Sin da Amurka a gefen taron G20 a Bali, ita ce zantawar da manyan jami’an ƙasashen biyu suka gudanar karo na 5 cikin wata guda, kuma wani muhimmin matakin diflomasiyya da zai ba da damar aiwatar da matsayar da shugabannin Sin da Amurka suka cimma a watan Nuwamban Bara.

Rahotanni sun nuna cewa, ministocin wajen Sin da na Amurka, sun shafe sa’o’i 5 suna tattaunawa, sun kuma zurfafa cikakkiyar musaya game da alakar dake tsakanin ƙasashen su, da batutuwan da suka shafi ƙasa da ƙasa, da na shiyya shiyya, da suke mai da hankali a kan su.

Cikin wadannan batutuwa, ɓangaren Sin ya fayyace matsayarsa cewa, sanarwa guda 3 da sassan biyu suka amincewa tun tuni, su ne babban ginshikin samar da kariya ga ƙasashen 2, waɗanda kuma su ne dukkanin duniya ke mayar da hankali a kan su.

Domin tabbatar da kyautata alaƙa da Sin, ya kamata Amurka ta ƙaurace wa furta magana ta kuma saba. Tarihi ya daɗe da tabbatar da cewa, nacewa aƙidu na gari wajen aiwatar da cudanyar ƙasa da ƙasa, shi ne matakin tabbatar da “samarwa kai kariya”, ƙarƙashin alaƙar dake akwai tsakanin Sin da Amurka.

Fassarawar Saminu