Mutanen ƙauyen Illela Babba, mai shekaru fiye da 200, na kukan rashin more dimukraɗiyya a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Al’ummar ƙauyen Illela Babba da ke a Ƙaramar Hukumar Mulkin Wamakko a Jihar Sakkwato na cigaba da nuna damuwarsu kan kasa shayar da su romon dimukuraɗiyya na samar masu da abubuwan more rayuwa, duk kuwa da irin gudunmawar da suke bayarwa na kai ‘yan siyasa a madafun iko.

Wakilin mu a Sakkwato, ya ziyarci ƙauyen na Illela Babba inda ya gane ma idonsa halin da mazauna ƙauyen ke ciki na rashin shayar da su romon dimokuraɗiyya, duk kuwa da cewa mulkin dimukuraɗiyya ake. Ga tsarabar da ya aiko mana:

Hanyar shiga Illela Babba

Tazarar ƙauyen na Illela Babba da babban birnin jihar Sakkwato dai bai wuce kilomita biyar, kasantuwar ƙaramar hukumar da ƙauyen ke ciki na daga cikin ƙananan hukumomi dake cikin birnin Sakkwato idan ka cire ƙananan hukumomin mulkin Sakkwato ta Kudu da ma ta Arewa.

A cewar hakimin ƙauyen Ummaru Alhaji Sani duk da ƙauyen ya shafe sama da shekaru 200 da kafuwa har yanzu ba su tava ɗanɗana romon mulkin dimukuraɗiyya ba.

“Ƙauyen nan an kafa shi ne shekaru 7 kafin kafuwar Sakkwato ta yanzu, gari ne mai ɗimbin tarihi da yawan jama’a, muna da rumfar zaɓe, muna zaɓen shugabanni a matakai daban-daban, amma duk da haka ba mu tava ɗanɗana romon mulkin dimukuraɗiyya ba a ƙauyen nan.

Mazaunin ƙauyen Illela Babba, Mustapha Aliyu

“Yawan al’ummar ƙauyen nan ya haura mutun 2,000, muna jefa ƙuri’a amma abin damuwar ‘yan siyasa ba su taɓa share mana hawayenmu ba, ka ga dai maƙabartarmu ta cika saboda rashin fili a nan muke sake bizne wasu idan aka yi rasuwa, ba wutar lantarki, kai saboda kawai mu mori ingantacciyar rayuwa muka haɗa kusan Naira 700,000 a lokacin gwamnatin Bafarawa muka janyo wuta daga ƙauyen Bakin Kusu dake makwabtaka da mu, amma ka ga wutar ko cajin waya ba ta yi, balle wani amfani na kasuwanci ko biyan buƙatun yau da kullum,” inji shi.

A cewar basaraken sun sha kai ƙorafi a ƙaramar hukuma da kamfanin siminti na BUA dake yake muna makwabtaka da shi amma har yanzu an rasa gwamnati ko kamfani da zai ji kukansu ya ɗan shayar da su romon dimukuraɗiyya.

“Haka a ɓangaren ruwan sha muke ta fama da wahalhalu iri daban-daban, bada wani mai hannu da shuni ɗan garin nan ya samar mana da rijiya da ake siyar mana da ruwa ba, wallahi da mun tagayyara saboda matsalar ruwan sha, ka dai ga yadda rijiyar mu take ba ruwa ga zurfi da sauransu; mu dai al’ummar ƙauyen Illela Babba muna cikin tsananin buƙatar taimakon mahukunta,” a cewarsa.

Babban masallacin Illela Babba

Shi ma wani mazaunin ƙauyen na Illela Babba Almuspha Aliyu da wakilin mu ya zanta da shi ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda aka maida su saniyar ware a shayar da su romon mulkin dimokuraɗiyya.

“Muna fama da matsaloli kusan 4 zuwa biyar, na farko akwai ta wutar lantarki, ga ƙarancin maƙabarta ta cika wani lokacin mutane har roƙo suke a ajiye masu wuri a makabartar koda ta Allah ta kasance gare su (mutuwa), ga rashin ayyukkan yi ga matasanmu. Ka duba ka ga tsakaninmu da kamfanin siminti na BUA bai wuce tafiyar ‘yan mintuna ba, amma ba mutum ɗaya tilo ɗan garin nan dake aiki a kamfanin siminti na BUA, muna ji yanda makwabtan ƙauyuka ke tada jijiyoyin wuya, mu akasin haka amma duk da haka ba a tava ɗaukar koda mutun guda ɗan ƙauyen nan domin ya yi aiki a kamfanin.”

Da yake malamin ya haura sama da shekaru 40, wakilin mu ya tambayesa, shin a shekarun da ko ya taɓa cin karo da wani aiki da aka yi da sunan gwamnati?

Taransfomar ƙauuen

Malam Almuspha ya kada baki yana cewa: “Ban cewa ba a yi ba, ban kuma cewa an yi, amma muna da aji ɗaya na makarantar Islamiyya wanda aka mana, amma da ba shi ba, duk da wutar NEPA ka ga yadda turakun ke batun faɗuwa, wutar ba ƙarfi wacce mune muka haɗa ƙarfi da ƙarfe amma ka ga kamar ba’a yi ba don ba ta tada fanka.”

Wannan dai na zuwa ne sa’ilin da ake cigaba da shagulgulgulan ranar dimokuraɗiyya a Nijeriya, lamarin da a cewar al’ummar ƙauyen sufa burin nasu a rayuwa bai wuce gwamnati ko ta jiha ko ƙaramar hukuma ba su share masu hawayen su.

“Muna da buƙatar a inganta mana wutarmu na sama mana cabubuwa, don waɗannan ita ce da kake gani ko yanzu aka yi iska mai ƙarfi suna iya faɗuwa, muna so a ƙara mana ƙarfin ta ko layi 3 ne haka,” inji malam Almuspha.

A nasa ɓangaren hakimin ƙauyen na ganin idan aka samar masu da ruwan sha, assibiti, ko makabarta tofa sukan ba za su taɓa manta gwamnatin da ta share masu hawayen nasu a tarihi ba.

Wurin ɗibar ruwa a Illela Babba

Duk ƙoƙarin da muka yi na jin ta bakin mahukuntan ƙaramar hukumar abin ya ci tura domin ɗan majalisar dake wakiltar ƙaramar hukumar a zauren majalisar dokoki ta jiha Murtala Bello Maigona ya bayyana cewa ba zai ce uffan kan lamarin ba, sai dai in tuntuɓi ƙaramar hukuma, kuma har zuwa lokacin haxa wannan rahoton da na kira mai kula da ita wayarsa a kashe.

Ƙauyen da ke gabas da kamfanin siminti na BUA dai na daga cikin tarin yankunan da mazauna garin ba su taɓa koda kurɓa romon mulkin dimokuraɗiyya ba, abinda a cewar Bashir Liman ɗaya daga cikin mazaunansa da gwamnati za ta samar masu da wani abun more rayuwa, tofa za su cigaba da tarairayarsa tamkar ƙwai.