2023: Tinubu ya zaɓi Kashim Shettima mataimaki

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa, Sanata Bola Tinubu, ya bayyana tsohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin wanda zai masa mataimaki a zaɓen na 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi sa’ilin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan ganawar sirrin da suka yi tare da Shugaba Muhammadu Buhari a Daura, Jihar Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Tinubun ya ziyarci Daura ne don miƙa gaisuwar Sallah ga Buhari da kuma neman haɗin kansa wajen ɗaukar Shettima a matsayin mataimaki.

A ranar Asabar da ta gabata aka ji Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya tsegunta cewa, Tinubu ya amince ya zaɓi mataimaki Musulmi.

Yanzu dai zaɓen Shettima a matsayin mataimaki da Tinubun ya yi, ya kawawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da ‘yan ƙasa ke yi game da batun Musulmi ko Kirista, wa zai yi wa ɗan takarar mataimaki.