RTEAN ta rantsar da shugabanninta reshen Abia

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Nijeriya (RTEAN) ta ƙaddamar da shugabanninta na reshen Jihar Abia.

Da yake jawabi wajen taron ƙaddamarwar wanda ya gudana a Abuja, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr. Musa Muhammed Maitakobi, ya yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar da aka rantsar a kan su haɗa kai su yi aiki tare don bunƙasa fannin sufurin jihar da ma na ƙasa baki ɗaya.

Maitakobi ya nusar da sabbin jagororin a kan su sani cewar, babu yadda za a yi wata ƙungiya ta samu cigaba ba tare da mamabobinta sun duƙule wuri guda sun yi aiki tare ba.

Ya ƙara da cewa, Shugaban RTEAN na Jihar Abia, Chief Nmandi Bologun ya yi jawabi mai matuƙar muhimmanci da ya ce ya yafe wa dukkan mambobin da suka yi masa laifi, inda shi ma ya buƙaci a yafe masa domin a tafi tare don amfanin RTEAN da ma jihar.

“Haɗin kai da cigaban mambobin RTEAN a Jihar Abia su muke buƙata, don haka ku koma gida ku haɗa kanku a tafi tare ba tare da nuna wariya ba…”inji Maitakobi.

A ƙarshe, mambobin ƙungiyar sun yi murna matuƙa da wannam cigaban da aka samu, tare da yaba salon jagorancin shugaban nasu na ƙasa, Dr. Musa Maitakobi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *