Goron Sallah: Adamu ya yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Andullahi Adamu (Turakin Keffi), ya yi wa Nijeriya fatan samun dauwamammen zaman lafiya.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ya fitar don taya al’ummar Musulmi murnar bikin Babbar Sallah.

Adamu ya miƙa saƙon goron sallar nasa ne a madadin jam’iyyarsa ta APC da kuma ahalinsa.

“Ina roƙon Allah ya ba mu ikon shaida bukukuwan Sallah masu yawa kuma cikin ƙoshin lafiya.

“Ya Allah, gare Ka kaɗai muka dogara don dawowar zaman lafiya a ƙasarmu, Ya share hawayen waɗanda matsalolin tsaro suka rutsa da su kana Ya sake haɗa su da ‘yan uwansu,” inji Adamu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *