
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawa ta tabbatar da Joseph Olasunkanmi Tegbe da Ambasada Enikanolaiye da a matsayin ministocin Tarayyar Nijeriya.
Ta tabbatar da nadin Ambasada Enikanolaiye a matsayin ƙaramin ministan harkokin waje da kuma Joseph Tegbe a matsayin ministan wutar lantarki.
Hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunayensu ga majalisar domin tantance su a matsayin manyan jami’an gwamnatinsa.
A yayin tantancewar, majalisar ta gargaɗi Tegbe akan matsalolin da ake samu a fannin wutar lantarkin Nijeriya, wanda ke buƙatar gagarumin gyara.
Da yake jawabin, Tegbe ya shaida wa sanatocin ce wajibi ne a sauya salon gudanar da fannin domin samun gyara mai ɗorewa, yana mai cewa za su bi matakan da suka dace wajen cimma nasara.
