
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Daɗaɗɗen ɗan nishaɗi, Charly Boy ya tunatar da taƙaddamar da aka yi tsakaninsa da tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha a shekarar 2014, inda ya kare matakin da ya ɗauka yayin faruwar al’amarin.
A wata hira da shi ta gidan talabijin, Charly Boy ya tunatar da lokacin da karɓe abin magana a hannun tsohon gwamnan yayin da yake tsaka da jawabi ga baƙin da suka halarci jana’izar mahaifin nasa.
A cewar Charly Boy, ya fahimci cewa an yi yunƙurin mayar da wajen taron wani fage na siyasa, lamarin da ya nuna ƙin amincewa a kai cikin yanayi na fushi.
“Mmhmm. Is that a crime? I for don slap am. He wanted to use my father’s burial as a campaign for politics. And you don’t do that. Not when I’m around”, inji shi kamar yadda ya faɗa cikin harshen turanci mai haɗe da yaren gida.
Charly Boy ya kuma yi iƙirarin cewa ya buƙaci Okorocha da ya fice daga wajen taron, yana mai turjiya akan tsohon gwamnan ya fahimci a ƙarƙashin ikonsa yake duk da cewa ya je taron da jami’an tsaron da ke ba shi kariya.
