Majalisar Dokokin Katsina ta buƙaci gwamnati ta gyara muhimman hanyoyi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A zaman majalisar dokokin na ranar ƙarƙashin jagoranci mataimakin kakakin majalisar Rt Hon. Abduljalal Haruna Runka, majalisar ta gabatar da ƙuduri na tunatar da ɓangaren zartarwa na gwamnatin jihar, kan buƙatar sake gina wasu muhimman hanyoyi da suka lalace domin sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziƙin al’ummomin da abin ya shafa.

A ƙudurin da Hon. Umar Ali Bindawa, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Bindawa, ya gabatar, inda ya buƙaci majalisa ta turawa ɓangaren zartarwa da ta sake gina hanyar Bindawa, Dallaje, Doro Geremawa zuwa Kwanar Duwan.

Hanyar wadda ta ratsa ƙananan hukumomin Bindawa da Mani. Ya bayyana cewa gyaran hanyar zai taimaka wajen inganta harkokin sufuri, kasuwanci da kuma rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta.

Kudiri na biyu Hon. Sha’aibu Zayyana Bujawa, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Mani, ya gabatar da ƙuduri kan buƙatar gaggauta gyaran hanyar Mani zuwa Dutsi, wadda ke haɗa ƙananan hukumomin Mani da Dutsi.

Ɗan majalisar ya ce lalacewar hanyar na jefa matafiya da masu safarar kayayyaki cikin matsaloli, tare da kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin yankin.

Bayan tattaunawa kan ƙudurorin, mataimakin kakakin majalisar ya buƙaci akawun majalisar ya turawa ɓangaren zartarwa da ta ɗauki matakan gaggawa wajen aiwatar da ayyukan sake gina da kuma gyaran hanyoyin domin amfanin al’ummar yankunan da abin ya shafa.

By ukarofi

Leave a Reply