Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji da warware matsalolin VAT

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilai ta amince da ƙudiri guda huɗu na neman gyaran fuska ga dokar haraji a Nijeriya da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

A lokacin da ya ke gabatar da rahoton nazari akan ƙudirin, Shugaban kwamitin majalisar kan kuɗi kuma jagoran kwamitin tantance ƙudirin, James Faleke, ya ce sun gudanar da aikin tantancewa mai zurfi tare da warware matsalolin da suka jefa al’umma cikin damuwa a karon farko da aka gabatar da shi.

Ya ce, an warware batutuwan da suka haifar da cecekuce game da abinda aka tara daga harajin VAT da tsarin kasaftawa, wanda an samar da tsarin bada kaso 50 ga jihohi da kuma kaso 35 ga ƙananan hukumomi.

Haka kuma, ƙudirin samar da hukumar haraji ta ƙasa, wanda ya ce sun yi gyara a kai ta yadda ba za a samu jagorori daga jihohi ba, ya na mai cewa za a zaɓo manyan daraktoci daga shiyyoyi shida na Nijeriya, waɗanda shugaba Tinubu ne zai naɗa su a matsayin tawagar jagorancin hukumar. Sannan za a yi zaɓin ne la’akari da bin jihohin ɗaya bayan ɗaya ta amfani da harufa.

Haka ma sauran ɓangarorin ƙudirin, waɗanda aka yi wa kwaskwarima game da gaɓoɓin da suka tada ƙura a baya.

Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas, ya ce wannan shi ne karo na farko da aka samu wani batu da ya samu goyon bayan baki ɗaya ƴaƴan majalisar, ya na mai yaba wa kwamitin kuɗi na majalisar da sauran masu-ruwa-da-tsaki daga shiyyoyin ƙasa da aka gayyato, waɗanda suka tsaya haiƙan wajen warware batutuwan da suka haifar da cecekuce.

By Babaji