
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu jami’an kula da zaman lafiyar al’umma a Edo, sun yi taƙaddama da wani direban motar kasuwa a Birnin Benin dake jihar, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar wata ƙaramar yarinya.
A yammacin ranar Laraba ne al’amarin ya faru a titin ‘Ring Road’.
Ya auku ne a lokacin da wani jami’in taskforce ya tunkari direban a salo na firgitawa bisa saɓa wa dokar hanya, inda jami’in ya yi ƙoƙarin kutsawa cikin motar.
Ganin yadda suka yi ƙoƙarin riƙe kan motar ya sanya direban fizgar motar a guje, wanda hakan ya sa ya rasa makama tare da murƙushe wata ƙaramar yarinya da ke tsaye a gefen titin a kusa da mahaifiyarta.
Shugaban Majalisar ‘Talakawa’ a jihar, Maxist Kola Edokpayi, ya koka game da faruwar al’amarin, ya na mai kira ga Gwamna Monday Okpebholo da ya gaggauta ɗaukar matakan gyara ga harkokin jami’an.
Tuni ƴan sandan jihar suka ce sun fara gudanar da bincike akan al’amarin.
