
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ta’addancin ƴan daba, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta jaddada batun haramta yin tashe da aka saba yi a kowane Ramadan a jihar.
Gwamnatin jihar ta yi hukuncin ne domin inganta kula da rayuka da dukiyoyin al’umma yayin da ɓata-gari suke amfani da hakan wajen farmakar mutane a gidajensu.
Rundunar ta gudanar da zama na masu-ruwa-da-tsaki a unguwanni don tattauna hanyoyin da za a bi wajen daƙile harin ɓata-garin.
Haka kuma, an bayyana shan miyagun ƙwayoyi a matsayin musabbabin samuwar harkar dabanci a jihar.
A sanarwar da Kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta yi kira ga jami’anta a sassan jihar daban-daban da su riƙa gudanar da sintiri wajen tsaftace unguwannin daga lalatattun mutane.
Ta kuma yi kira ga al’umma da su bai wa jami’an haɗin-kai waje aiko da duk wani rahoton abin zargi da suka gani a yankunansu ta lambobi kamar haka:
08032419754
08123821575
09029292926
Rundunar ta kuma jaddada aniyarta ta tabbatar da bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kulawa gami da yin godiya a gare su bisa haɗin kai da suke ba su.
