
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga haɗin kai tsakanin jagorori wajen tallafa wa ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na yin gyaran fuska a Nijeriya.
Shettima ya yi kiran ne a yayin taron shan ruwa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a Fadar shugaban ƙasa, wanda aka gayyaci jagororin Majalisar Dattawa.
Ya ce, Nijeriya ta kai matakin da jagorancin Shugaban ƙasar da tsare-tsarensa sai sun samu aiwatarwa bisa inganci domin samun sauyi mai ɗorewa, ya na mai cewa ƴan Nijeriya sun fara ganin alfanon haka a saukar farashin abinci da fetur da kuma kasuwar zamani.
Shettima ya kuma ce, tattalin arziƙin ƙasa ya hawu da kaso 4.6 daga 4.3 a shekarar 2025, ya na mai jinjina nasarar da hangen nesan Shugaba Tinubu bisa matakan da ya ke bi.
Ya yi kira ga jagororin ƴan siyasa da su haɗa hannu don ci-gaban ire-iren waɗannan ayyukan gyara da Shugaban ƙasar ya sanya a gaba, inda ya ce haɗin kai yana da muhimmanci wajen ciyar da ƙasa gaba.
Kazalika, mataimakin shugaban ƙasar ya yaba wa majalisar kan haɗin kanta ga shugabancin ƙasa, ya na mai kira ga ƴaƴanta da su riƙa ganin kawunansu a matsayin ƴan gida ɗaya ba tare da la’akari da banbance-banbancen siyasa ba.
