Gidauniyar Hassana Isah ta raba wa marayu kayan Sallah kyauta 

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Gidauniyar Hassana Isah dake ƙaramar Hukumar Malam Marori ta rabawa marayu da marasa galibu 450 rigunan sawa a matsayin kayan Sallah da za su yi bukukuwan Sallah azumi a ƙaramar Hukumar Malam Madori dake Jihar Jigawa. 

Kimanin marayu 450 ne suka ci moriyar kayan da aka raba tare da yara marasa galibu da aka raba masu yadika domin ɗinkin sallah mai zuwa. 

Mai bai wa gwamna shawara akan harkokin mata da ilimi, Hajiya Hassana Isah ta tabbatar da faruwar labarin jim kadan bayan rabon kayayyakin da gidauniyarta ta yi a ƙaramar Hukumar ta Malam Madori dake cikin yankin Masarautar Hadejia. 

Ta ce gidauniyar tata mai suna Hassana Isah Lalala and Family a ƙarƙashin kulawarta ta raba kayayyakin ne ga yara ‘yan shekaru biyar zuwa sha uku waɗanda mafiya yawansu marayu ne da ‘ya’yan marasa ƙarfi.

Da take jawabi akan dalilanta na fito da wannan tsari, ta ce ta ɓullo da tsarin ne da nufin tallafawa marayu da yayan marasa ƙarfi su sami damaryin walwala a lokacin da akeyi bukukuwan sallah kamar yadda masu iyaye zasu gudanar da nasu bikin sallar.

Da yake jawabi a wajen rabon kayan hakimin Malam Madori Dokajin Hadejia Alh Muhd Sale Kuliya ya yaba wa gidauniyar bisa hangen nesanta tare da nuna halin ya kamata akan marayun da ‘ya’yan marasa gata a ƙoƙarin gidauniyar na farantawa marayu da ‘ya’yan marasa ƙarfi.

By ukarofi