
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin wucin-gadi kan binciken badaƙalar hukumar bogi (PFIPC) na Majalisar Wakilai, ya bayyana cewa wasu manyan jami’an gwamnati sun kasance amintattun hukumar gudanarwarta duk da tambayoyi akan halascinta da dokance.
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi ne ya bayyana hakan a wata hirar bincike a ranar Alhamis, inda ‘yan majalisa suka ƙalubalanci Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), Shehu Mohammed kan amincewa da bayar da alunan lamba na ababen hawa guda bakwai da aka danganta su da hukumar.
Gagdi ya ce, waɗanda aka zayyano a matsayin amintattun sun haɗa da Shugaba Bola Tinubu, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume; Ministan Abuja, Nyesom Wike; Shugabar Ma’aikatar Ma’aikata; Gwamnan Babban Bankin Nijeriya da kuma Antoni Janar na Ƙasa.
Sauran waɗanda aka zarga sun haɗa da ministoci masu sanya ido kan lamuran kuɗaɗe, sufurin jiragen sama, noma da tsaron abinci, cikin gida, kasafi da shirye-shiryen ƙasa,, ruwa da tattalin arziƙi na zamani, harkokin ‘yan sanda, sufuri, ayyuka da kuma lantarki.
Kwamitin ya ƙalubalanci FRSC kan rashin bincike akan sahihancin takardun da hukumar bogin ta miƙa mata, musamman wata takarda da aka zargi Shugaban da wasu mambobin Majalisar Zartarwar ta Ƙasa (FEC) a matsayin ‘yan kwamitin amintattun.
Haka kuma, Gagdi ya koka kan yadda takardun da PFIPC ta gabatar ba su da sahalewar wata cibiyar gwamnati a hukumance kuma FRSC ta karɓe su daga hanyoyin tantancewarta.
