Makamashi: Tallafin man fetur

Tare Da BASHIR MUDI YAKASAI

Ga Malam Bahaushe, ma’anar tallafi yana fassara karin maganar nan da ke cewa,”hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka”. Ma’ana, dukkan wani abu na alheri ba ya yiwuwa sai da kama-kama na jama’a, kamar yadda ake yi a lokacin bukukuwa, inda ake yin ajo a tara wa ma’aurata kuɗi, domin tafiyar da biki cikin nishaɗi da walwala.

Haka ake tallafa wa mai rauni a cikin jama’a lokacin faɗuwar damina, inda jama’ar gari suke zuwa gonaki, domin tallafawa tun daga sassabe zuwa shuka, noma har izuwa furfure, idan kuma kaka ta yi, a tallafa wajen kwasar amfanin gona zuwa gidaje.

Saboda haka, tallafi ba sabon abu ba ne ga rayuwar Malam Bahaushe. Gwamnatoci tun daga mulkin sarakuna har izuwa mulkin Turawa ’yan mulkin mallaka da kuma Jamhuriya Ta Farko ƙarƙashin Abubakar Tafawa Ɓalewa da Nnamdi Benjamin Azikiwe, waɗanda suka yi mulki daga 1963 zuwa 1966, suke ba wa talakawan ƙasa tallafi a harkar noma da kiwo, wanda Nijeriya ta karɓi gaba a wannan fanni a faɗin duniya, amma tun daga kasuwar man fetur ta kankama, manyan kuɗaɗe suke shigowa ƙasa, aka shiga sharholiya da wadaƙa, aka shiga cin duniya da tsinke a Nijeriya.

Hakan ya haifar da matsaloli masu tarin yawa, wanda ya kawo sauyin gwamnatoci daga soja zuwa soja ko daga soja zuwa farar hula. Wani abin sha’awa shine, tun daga Jamhuriya ta Huxu a ƙarƙashin Cif Olusegun Matthew Okikiola Ogunboye Aremu Obasanjo, wacce ya yi mulki daga 1999 zuwa shekara 2007, a wannan lokaci ne da aka haifar da gurɓataccen shugabanci na haɗin kai da ’yan baranda na ƙasashen waje wajen wawure dukiyar ƙasa da yi wa manufar ƙasa karan-tsaye da gurgunta ’yancinta ta kasance ’yar amshin shata na waɗansu ƙasashen duniya ta bakin Bankin Duniya da Hukumar Lamini ta Duniya, wato IMF, da kuma ƙungiyar nan ta G7, wato ta ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki da ƙungiyar G20, wacce Nijeriya ta na ciki, waɗanda suke fito da tsare-tsare na yadda za su cigaba da mallakar duniya ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar al’umma.

Su ne suke tsara sharuɗɗa na yadda al’ummar duniya za ta tafi da al’amuranta har da wannan batu da muke tsokaci a kansa, wato tallafi kan makamashin man fetur da gas da kalanzir da makamashin da jiragen sama da na ruwa da kuma jiragen ƙasa suke amfani da su.

Kowanne daga cikinsu ƙasashen duniya sun dogara kacokan a al’amuransu na sufuri da wutar lantarki da masana’antu manya-manya da ƙanana. Muhimmancin makamashi ga rayuwar bil’adama suna tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da abinci da ruwan sha.

Rashin makamashi annoba ce ga rayuwa, musamman a wannan zamani da aka ɗora duniya bisa tafarkin bunƙasar tattalin arziki. Al’ummar duniya ta na ganin mutuncin ƙasa ta samun kuɗaɗen shiga ga ƙasa, wato ‘Gross Domestic Product’ (GDP) da kuma ’yan qasa nawa suke samu daga arzikin da take samu, wanda ake kira da ‘GDP Per Capital’; wanda ƙididdiga take nunawa cewa, ’yan Nijeriya sama da kashi 70% suna rayuwa a ƙasa da Dalar Amurka ɗaya a kullum, wato dai a ƙiyasi, ’yan Nijeriya ba sa samun sama da Naira 600 kenan a kullum. Saboda haka, ga magidanci da yake da mata guda da ’ya’ya uku kuma a gidan haya a birnin Kano ko Sokoto ko Maiduguri ko Badun ko Ikko ko Fatakwal ko Kalaba ko kuma Inugu, ta yaya zai rayu cikin walwala da kwanciyar rai?

Don haka sai fatara da talauci da Yunwa da kuma jahilci sai suka sami gindin zama. Cikin ƙanƙanin lokaci sai rikice-rikice na addinai da ƙabilanci da rashin jituwar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tsakanin Fulani makiyaya da manoma da kuma rigingimun masunta da sarakunan ruwa suka yi ƙamari. Hassada kan rabon dukiyar ƙasa ta kunno kai. Nan da nan kuwa sai ta haifar da ƙungiyoyin ƙabilanci irin su MASSOB da Bakassi Boys da OPC da MEND, waɗanda suka ɗauki makamai suna kashe bayin Allah ba su ji ba ba su gani ba.

Mutane da dama sun faɗi albarkacin bakinsu na dalilan da suka haifar da rikicin Boko Haram da cigaba da rura wutar rikicin da kuma yadda abin ya yaɗu kamar wutar daji. Wasu masu fashin baƙin al’amuran yau-da-kullum sun ce, ba zai yiwu a ce almajiran Marigayi Malam Muhammadu Yusuf, wanda jami’an tsaron ƙasar nan suka kashe tare da wasu muƙarrabansa ba tare da gurfanar da su gaban shari’a ba, wanda ’yan uwansa suka harzuƙwa wajen neman a yi musu adalci, shi ya ingiza wutar wannan rikici.

Maganar gaskiya talauci da ƙarancin ilimi na addini da ilimi na zamani da rashin aikin yi ga magidanta da kuma matasa maza da mata da rashin girmama buƙatun ƙasa sune suka haddasa rikicin Boko Haram a namu tunanin.

Soboda abin takaici, tun 1973 da shugabanni na wancan lokacin suka ga dacewar su samar da tallafi kan man fetur da dangoginsa, dalilin tashin gwaron zabi da farashin man fetur ya yi a faɗin duniya, inda ya haifar da faɗuwar tattalin arziki na ƙasashe masu tasowa irin Nijeriya, inda rayuwa ta ƙuntata, saboda tashin farashin kayayyakin masurufi, wanda al’umma ke buƙata.

An samar da wannan tallafi na man fetur da dangoginsa a Nijeriya da nufin kawo sauƙi ga ’yan ƙasa a dukkan fannonin rayuwa.

Tallafin shine sayar da man fetur da dangoginsa ƙasa da farashin kasuwar duniya. Sannan samar da sauqi ga kuɗaɗen fito, wato dai Nijeriya za ta ɗauki nauyin kuɗaɗen dako daga inda aka sauke man a daffo da kuma guraren tace su a Fatakwal da Warri da Kaduna. Wato dai farashi daidai da na Kalaba da Ikko da Abuja da Kaduna da Sokoto da kuma Maiduguri da duk wani ƙauye da ke Nijeriaya babu ƙarin ko Sisin Kwabo ga duk wanda ya je gidan mai.

Gwari-Gwari, a bisa wannan tsari, duk ɗan Nijeriya zai amfana daga wannan tallafi, saboda sauƙi na sama da kashi 1000 na farashin kayayyaki da yakamata ya biya, amma saboda wannan tallafi daga man fetur da dangoginsa, wato gas na girki da kalanzir da takin zamani da man shafawa da sabulun wanki da na wanka da kayan ƙarau (ceramic) da robobi da takardu da za a yi littattafan ’yan makaranta da siminti na gine-gine da tufafi da muke sanyawa, wato ‘textiles’. A taƙaicen taƙaitawa, babu wani abu da ’yan ƙasa ba sa amfana daga wannan tsari na tallafi, amma tambayar ita ce, shin haka abin yake a Nijeriya?

Saboda muhimmancinsa duk duniya, musamman ma ƙasashen da suke haƙo wannan kadara ta man fetur da dangoginsa suke ba wa al’ummominsu wannan tallafi, misali Ƙasar Amurka tana kashe sama da Dalar Amurka Biliyan 500 a duk shekara, haka Ƙasar sin, wato Chana, ta na kashe sama da Dalar Amurka Biliyan 700 a tallafi, ita kuwa Ƙasar Saudi Arabia na kashe sama da Dalar Amurka Biliyan 29, ita ma Indiya na kashe Dalar Amurka biliyan 22. Amma babban abin sha’awa shine, waɗannan tallafi yana zuwa ga talakawan ƙasarsu.

Abin takaici a Nijeriya, da ke da mutane sama da miliyan 220, mutane da ba su kai dubu ba su kaɗai suke wawure kuɗaɗen, kuma su yi babakere da dukkan biliyoyin daloli da aka ware domin tallafi, su kaɗai daga su sai ’ya’yansu, sauran ‘yan ƙasa ko oho!

Wannan shi ya haifar da halin da muke ciki na rashin tabbas. Shi ya sa a ranar Litinin, 29 ga Mayu wannan shekara ta 2023, Mai Girma Shugaban Ƙasa, Ahmad Bola Tunubu, ya soke wannan tallafi kwata- kwata.

Duk wanda ka ji yana sukan wannan manufa, to ka tabbata ɗan baranda ne. Wato ejen na waɗannan kaskoki masu raɓar talaka suna zuƙar jininsa, su ne ke so a cigaba da wannan rashin adalci.

Idan ku ka biyo mu a mako mai zuwa, za mu zo muku da hujjoji na yadda suke kwasar ganima da sunan dillalan man fetur da dangoginsu. ’Yan ƙasa da kuma kamfanonin ƙasashen waje, ku biyo mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *