Makarantar PADWO ta yaye ɗalibai 264 a karon farko

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Makarantar PADWO da ke ƙarƙashin wata ƙungiyar mai rajin tallafawa marasa lafiya da marasa galihu da ke garin Argungu a jihar Kebbi ta yaye ɗalibai 264 da suka kammala karɓar horo kan aikin kiwon lafiya na matakin shaidar satifiket da kuma difloma a sassa daban-daban a karon farko bayan kafa ta a shekarar 2021.

Da ya ke jawabi, shugaban ƙungiyar Dokta Garba Hassan Mustapha Ɗan Balarabe ya bayyana cewa wannan aikin ya soma ne daga ƙungiyar taimakawa marasa lafiya da ba su da galihu tun shekarun baya sai dai bayan tuntubar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya bayar da shawarar ya kamata a buɗe makaranta don koyar da aikin kiwon lafiya inda kuma ba tare da ɓata lokaci ba aka soma neman yadda za a fara a shekarar 2020 kuma cikin ikon Allah a ɗan ƙanƙanin lokaci aka sami nasara har yau ga shi an yaye ɗalibai 264.

Ya yaba wa ‘ya’yan asalin ƙasar masautar Argungu da ke bayar da gudummawa don samun nasarar wannan makarantar.

Ya kuma nemi gwamnatin jihar Kebbi da ta yi ƙoƙarin samar da gurabun aiki ga ɗaliban da suka kammala karatu a irin waɗannan makarantar a irin wannan lokacin da ke akwai ƙarancin ma’aikatan lafiya a sibitoci.

Kwamishinan lafiya Alhaji Sama’ila Yakubu Augie a madadin gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya yaba wa waɗanda suka ƙirƙiro wannan makarantar ya kuma yi kira ga ɗaliban da suka kammala karatu da su ja ɗamara su shirya zama jakadu nagari a duk inda suka sami kawunan su.

Gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris mutum ne da ke bayar da kulawa ta musamman ga harkokin lafiya wanda mutanen Argungu da Augie da Kangiwa da kuma Kamba shaida ne saboda manyan asibitocin da su ke da su an gyara su kuma duk faɗin jihar nan ana nan ana gyaran manyan asibitoci, waɗansu kuma an gama, yayin da ƙananan asibitoci su ma ba a bar su baya ba.

Ya bayyana cewa gwamnatin za ta zauna tare da shugabannin gudanarwa na wannan makarantar don ganin yadda gwamnatin za ta shigo ta bayar da na ta gundumawa.
Ya kuma yaba wa ɗaiɗaikun mutanen da ke tallafa wa wannan ƙungiyar ta PADWO wajen ganin ta sami nasarorin aiwatar da ayyukan ta.

Bayan taron dai har wa yau dai ƙungiyar ta PADWO ta karrama waɗansu fitattun mutane da dama bisa ga gidummawar su ke bayarwa a masarautar Argungu baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply