
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ƙaryata zarge-zargen Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) cewa ya kwafi wani yanki na bayanan kuɗaɗen almundahanar gwamnatin Janar Sani Abacha da aka gano, waɗanda adadinsu ya kai kimanin Dala miliyan 310, inda daga bisani suka haura zuwa miliyan $322.5 da riba (interest).
A wata takarda daga mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Doka ya fitar, Malami ya yi watsi da ikirarin idna ya ce zancen ba gaskiya ba ne saidai abu ne da kaa ƙirƙira domin rufa-rufa ga ainihin gaskiyar al’amarin.
An ruwaito cewa EFCC ta zargi Malami da cewa ya musanya hanyoyin gano kuɗaɗen waɗanda tuni Lauyan Switzerland, Enrico Monfiri ya kammala aiki akansu tun kafin Malamin ya kama aiki a 2015.
To saidai Malami ya musanta ikirarin wanda ya bayyana a matsayin ƙarya, inda ya ce babu wasu kuɗaɗe da suak shiga asusun tarayya da sunan waɗanda aka gano.
Ya kuma ce, hatta matsayar Mista Monfiri sai da ta ci karo da abin da EFCC ta yi ikirarin, wadda ya aike wa gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari a 2016.
Malami ya ƙara da cewa, Monfiri ya nemi a ba shi kafin alƙalami Dala miliyan 5 da kuma kaso 40 wanda daga bisani ya mayar da shi kaso 20, lamarin da gwamnatin Nijeriya ta ƙi amince wa.
Har’ilayau, tsohon ministan ya ce ya sanya ido akan kuɗaɗen da aka yi almundahanarsu a gwamnatin Abacha, waɗanda suka haɗa da Dala miliyan 322.5 Daga ƙasar Switzerland (2017-2018) da aka raba su a tsarin Conditional Cash Transfer ƙarƙashin kulawar Bankin Duniya da kuma Dala miliyan 321 daga Jersey a (2020) da aka ware domin muhimman ayyukan more rayuwa ciki har da babban titin Legas zuwa Ibadan, Abuja zuwa Kano da gadar Neja ta biyu.
