
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su taimaka mata wajen sanya ido akan kiyaye umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye ƴan sanda daga gadin manyan mutane.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara akan harkar yaɗa labarai, Daniel Bwala ya yi wannan magiyar a wata hira da gidan talabijin na TVC a jiya Lahadi, inda ya bayyana ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya take yi wajen ganin an kiyaye umarnin Shugaban ƙasar, yana mai kira ga jama’a da su ruwaito duk wanda aka samu da saɓa wa hakan ta hanyar ɗaukar hoto ko bidiyon al’amarin.
Ya kuma ce, janye jami’an ƴan sandan ba dukkan jami’an gwamnati ya shafa ba, saidai akwai wasu daga cikin gwamnatin da aka amince jami’an tsaro su yi gadin su na daga jami’an ko na wasu hukumomi.
Ya ƙara da cewa, jami’an hukumomin DSS ko na Cibil Defense ka iya bada kariya a wuraren da ya zama wajibi, “amma ƴan sanda ba su da alaƙar kasancewa tare da ku”, inji shi.
Umarnin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin wajen amfani da harkokin ƴan sanda yadda ya dace da kuma tabbatar da mayar da hankali akan zaman lafiyar al’umma a madadin bada kariya ga manyan mutane.
