
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani magidanci, matarsa da ƴaƴansa uku run rasu a yayin da gobara ta kama gidansu da ke yankin Ƙofar Sauri acikin garin Katsina, Jihar Katsina.
Al’amarin ya faru ne a safiyar yau Litinin, wanda ya yi sanadin ƙonewar kusan dukkan kayayyakin da ke cikin gidan.
Wani shaida da ya nemi a sakaye sunansa ya al’amarin auku ne jim-kaɗan bayan dawo da wutar lantarki a unguwar.
A cewarsa, an samu tartsatsin wuta a wasu layukan lantarkin, wanda ta yiwu shi ne sanadiyyar kamawar gobarar.
Ya ƙara da cewa, sanannen al’amari ne cewa ba a tashi gyaran wuta sai cikin dare sosai, sannan kuma a kan kawo wuta mai ƙarfin da ya wuce kima.
Duk da cewa ana ganin yanayin sanyi na daga cikin dalilan da suke sabbaba gobara, wani mazaunin yankin ya kiraye hukumomi da su ƙaddamar da bincike akan gano musabbabin faruwar al’amarin.
A wani labarin kuma, Gwamna Umaru Dikko Raɗɗa na jihar ya riski munanan haɗurra biyu a ranar Lahadin yayin da yake komawa gida daga ziyararsa aiki a yankin Funtua.
A cewar sanarwar Sakataren yaɗa labaransa, Kaula Mohammed ya fitar, al’amuran sun faru ne jim-kaɗan bayan kammala ayyukansa a Ƙaramar Hukumar Matazu, lamarin da ya sa gwamnan ya tsayar da tawagarsa tare da tabbatar da sanya ido akan kuka da waɗanda iftila’in ya rutsa da su.
