
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma sun shiga firgici a ƙauyen Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara sakamakon awon-gaba da wani mazaunin yankin a jiya Lahadi.
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da aka sako masu bauta 38 da aka sace a wani coci a garin a makon da ya gabata.
An gano cewa, maharan sun kutsa wata gona da ke kan hanyar Eruku zuwa Koro da tsakar rana. Haka kuma, su huɗu ne suke je ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 da adduna.
Wani jagoran al’umma da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ƴan bindigar sun shiga yankin ne a lokacin da ake tsaka da aiki, inda suka tafi da wani mai suna Annas Aasanru.
Kwara na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar garkuwa da mutane a ƴan kwanakin nan inda aka yi wasu munanan hare-hare guda biyu acikin mako guda.
A kwanakin baya ne ƴan bindiga suak shiga ƙauyen Eruku tare da yin awon-gaba da mutane 11 waɗanda bakwai daga cikin su ƴan gida ɗaya ne.
