Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, ta hannun Shirin Kano state Special Agro-Processing Zone (SAPZ) na Jihar Kano tare da haɗin gwiwa da IFAD, ta gudanar da taron ranar nuna fasahar noman shinkafa a Tungar Chiromawa Garin Babba, da ke ƙaramar hukumar Garin Malam, Kano domin tantance ci gaban aikin gona a cikin zagayen bincike na biyu na FGN/SAPZ/IFAD.
Babban jami’in SAPZ na jihar Kano, Malam Aminu Iliyasu, ya ce an shirya taron ne domin bai wa manoma damar koyo da ganin sabbin fasahohin noma da za su inganta amfanin gona, tare da rage asarar bayan girbi da buɗe sabbin kasuwanni.
Manoma sun kalli gwaje-gwajen noma mai jure canjin yanayi, ingantattun iri, taki, ban ruwa, yaƙi da ƙwari da kuma dabarun bayan girbi.
A yayin taron, SAPZ ta raba kayan noman rani ga manoma 9,870 a ƙananan hukumomin Garin Malam, Gezawa, Bichi da Bagwai, ciki har da irin FARO 44, takin Urea da NPK, da magungunan ƙwari, domin bunƙasa noman shinkafa a daminar 2025.
Masana sun koyar da manoma muhimman matakai tun daga tantance fili, gyaran ƙasa, nersari, shuka daidai, amfani da taki, kula da ciyawa, tsarin gudanarwa tun daga tushe da kuma kula da ruwa.
Kazalika an kuma ja hankalin su kan girbin shinkafa a lokacin da ya dace da busar da wuri zuwa danshi mai kyau domin ajiya.
Jami’an shirin sun bayyana ƙwarin gwiwa cewa tallafin SAPZ zai ƙara yawan amfanin shinkafa a Kano, tare da ƙarfafa juriya kan matsalolin yanayi da samar da ƙarin kuɗin shiga.
Huwaila Shuaibu Ibrahim ɗaya ce daga cikin waɗanda suka amfana, da horon na SAPZ ta bayyana cewa SAPZ ta taimaka masu matuƙa, tace domin ada idan sun yi noma ba ruwansu da binciken wurin noma, to amma yanzu da SAPZ ta koya masu yadda ake binciken wuri kafin a yi shuka.
Ta ce, “Sai mun je mun ga gurin idan zai karɓi irin to shikenan idan ba zai karɓa ba to sai mu haƙura, don haka yanzu a bana mun Noma FARO 44”
“A baya idan mun noma eka ɗaya muna samun buhu 20 zuwa 25 amma a yanzu bayan wannan horo da aka bamu yanzu muna samun buhu 35 zuwa 40”. inji Huwaila.
