Daga JOHN D. WADA a Lafia
An shawarce masu harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan baki ɗaya su zuba jari sosai a fannin fasahohi domin su taimaka musu wajen ɗorewar harkokinsu na kasuwanci da kuma inganta ayyuka da nasarori.
Shawarar ta fito ne daga wani malami a sashen gudanar da kasuwanci na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Barnabas Embugus Barde.
Farfesan ya kuma shawarce su da su riƙa koyar da ma’aikatansu yadda za su yi amfani da sabbin fasahohin zamani yadda ya kamata, domin taimaka wa kasuwancinsu kawar da tsofaffin dabaru da kuma samun karin yawan aiki cikin inganci.
Malamin ya bayar da wannan kira ne a ranar Laraba yayin bikin gabatar da lacca ta 56 a jami’ar, wanda ya gudanar, kuma shugabanni da ma’aikatan jami’ar da dama sun halarta.
Yayin jawabi a laccar da taken ta: “Gudanar da Kasuwanci a Zamanin Dijital: Fahimtar Tasirin Kasuwanci, Basirar Na’ura (AI), Robotoci, Nazarin Bayanai, da Zuba Jari,” Farfesan ya ce wajibi ne a tabbatar ba a take haƙƙin ma’aikata ko jin daɗin su ba.
A cewarsa, dole ne kasuwanci su fahimci damar da kowace fasaha ke ɗauke da ita da yadda za a yi amfani da su wajen samar da sabbin damar kasuwanci da kuma kasancewa masu gogayya. Ya ƙara da cewa ya kamata su fahimci ƙalubalen da za su iya fuskanta a kowanne fanni, tare da yin shirin zuba jari a bincike da ci gaban fasaha, gwaji da ƙirƙire-ƙirƙire.
Yayin magana kan “Barde Model” a fannin kasuwanci, Farfesa Embugus Barde ya ce yana da gagarumar tasiri wajen dabarun kasuwanci, gudanarwa da ayyuka, kuma yana iya haifar da ingantaccen yanke shawara, ƙaruwar aiki da inganci, yawan riba da kuɗaɗen shiga, da kuma kyakkyawan tsarin magance haɗari.
Sai dai ya bayyana cewa akwai batutuwan maye gurbin ma’aikata, kariyar bayanai da tsaro, da wasu muhimman batutuwan ƙa’idoji da ya kamata a kula da su.
Ya jaddada kamar haka:
“Kasuwanci na iya amfani da nazarin bayanai wajen ƙirƙirar kamfen na talla kai tsaye ko amfani da AI da robotoci wajen samar da sabbin kayayyaki da sabis.
“Wannan muhimmanci ne matuka duba da cewa basirar na’ura da robotoci suna karɓe ayyukan mutane a hankali. Dole mu shirya wa ƙalubalen da ke tafe. Haƙiƙa, artificial intelligence tana karɓe ayyukanmu.
“Robotoci suna karɓe ayyukanmu. Saboda haka idan akwai wani abu da ya shafi irin wannan batu, don Allah dole mu farka da cikakkiyar wayewa.
“An shawarci ma’aikata su riƙa koyon sabbin ƙwarewa da dabara da za su taimaka musu. Ta haka kasuwanci za su fi samun damar tafiya da tsarin Barde model da kuma cin gajiyar damar da yake ƙunshe da ita.
“Kasuwanci yakamata su yi nazari sosai kan amfanoni da kalubalen da ke tattare da haɗa waɗannan fasahohi a ayyukansu, sannan su ɗauki matakai masu kyau don magance haɗari tare da cin gajiyar fa’idodin da ke akwai.”
Farfesa Barde wanda ya dage cewa ana iya amfani da fasahar kirkire-kirkire (entrepreneurship) wajen samar da sabbin dabarun kasuwanci da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ta fuskar fasaha, ya ƙara da cewa yana da kyau a lura cewa Barde model na iya yin tasiri sosai a kan ma’aikata domin yana iya haifar da rasa aiki da kuma buƙatar sabbin ƙwarewa da fasaha.
Tun farko a jawabin maraba na shugaban babban jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman wace ta samu wakilcin mataimakin ta a fannin ilimi a jami’ar wato farfesa Ari Maikano ya bayyana mai gabatar da laccar a matsayin ƙwararren da ya daɗe yana bada gagaruman gudumawa ba a jami’ar ta Nasarawa kaɗai ba har da ƙasar nan baki ɗaya musamman a fannin harkokin kasuwanci inda yake koyarwa inda tace tabbas idan za a yi amfani da abubuwa dake cikin laccar za a iya magance matsaloli da dama a kasar nan baki ɗaya musamman waɗanda suka shafi kasuwanci da sauran su.
A ƙarshe dai an baiwa Farfesa Barnabas Barde lambar yabo ta musamman da ɗaukan hotuna da sauran su.
