
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sabon faɗi in faɗa na neman kaurewa yayin da Umar D. Duhu, wanda tsohon mamban kwamitin ayyuka ne na jam’iyyar APC ya mayar da martani ga Dakta Hakeem Baba-Ahmed, wato tsohon mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa bisa neman Tinubu ya sauka a mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa Baba-Ahmed ya bayyana ƙarara cewa kada Shugaba Tinubu ya sake neman tsayawa takara a karo na biyu, wato a zaɓen 2027, saboda a cewarsa, shugaban ƙasar bai ɗauko hanyar magance matsalolin Nijeriya ba.
Ya ce, Tinubu ya cimma burin rayuwarsa na zama shugaban ƙasa, amma kuma ba ya gudanar da jagorancinsa yadda ya dace.
Ya kuma shawarci shugaban ƙasar da ya janye batun sake neman zaɓe ga na ƙasa da shi ta fuskar shekaru kuma mai lafiya ta yadda zai zama mai ba shi shawarwari a bayan fagen.
Kalaman nasa na zuwa ne duk da cewa jam’iyyar APC ta amince Tinubu ya sake tsayawa takara a karo na biyu tun a watan Mayu.
Saidai, Umar D. Duhu a ɗaya gefen ya ƙi goyon bayan Baba-Ahmed a wannan batun inda ya ce hakan rashin ƙwarewa da haddasa rikita-rikita ne a harkokin siyasa.
Ya bayyana cewa, rashin shawo kan matsalolin Nijeriya a yanzu ga Shugaba Tinubu ba gazawa ba ce, saidai akwai buƙatar a yi la’akari da yawansu, waɗanda sai an ba su wadataccen lokaci.
Kazalika, Duhu ya zargi wasu manya a Nijeriya da ƙoƙarin karkatar da hankalin al’umma daga matsalolin da ke damun su musamman tsaro, lamarin da ake ta ƙoƙarin siyasantarwa.
