Mambobin APC sama da 200 sun sauya sheƙa zuwa PDP a Jigawa 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Aƙalla mambobi 289 na Jam’iyyar APC mai mulki sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP a  mazaɓar Sakwaya, ƙaramar Hukumar Dutse, jihar Jigawa.

Jaridar Manhaja ta rawaito cewa taron sauya sheƙar ya gudana ne a ranar Juma’a a ofishin PDP na mazaɓar, inda mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha, Umar Danjani, ya wakilci shugaban jihar wajen tarbar sabbin mambobin.

ɗanjani ya yaba wa fitattun ‘yan adawa da suka fito daga sassan jihar don halartar taron, yana mai bayyana sauya sheƙar a matsayin babban ƙarfafawa ga jam’iyyar wajen samun haɗin kai da ƙarfi gabanin zaɓe.

Ya jaddada cewa jam’iyyar PDP a buɗe take tare da shirin tallafawa sabbin mambobin wajen shiga cikakken aiki a jam’iyyar, tare da alkawarin kara wayar da kan jama’a a matakin tushe da ƙara haɗa kan jama’a gabanin zaɓen 2027.

Ya kuma buƙaci dukkan ‘yan siyasa a jihar su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da mutunta ɗabi’un dimokuraɗiyya yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙaruwa.

ɗanjani ya yi alƙawarin cewa jam’iyyar za ta samar da dukkan goyon baya da ake buƙata domin tabbatar da shigar sabbin mambobin ba tare da wata matsala ba, yana mai cewa:

“Muna maraba da ku hannu bibbiyu tare da alƙawarin yin aiki tuƙuru wajen magance matsalolinku yayin da muke gina Jigawa mai ƙarfi tare.

“ƙofarmu a buɗe take ga duk wanda yake da kishin ci gaban Jigawa. Da zuwanku, muna ƙara matsowa kusa da samun haɗin kai na gaskiya da zai kawo ci gaba mai dorewa a jihar.”

By ukarofi