Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan yunƙuri na kamfanin ya biyo bayan da yanayin tsaro ya inganta a jihar kamar yadda Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗa.
Gwamna Raɗɗa Ya bayyana hakan ne a yayin taron haɓaka tattalin arziki da zuba hannun jari da ya gudana a Katsina.
A yayin taron, kamfanoni daban daban na faɗin Najeriya za su zuba hannun jari tare da sa hannun ƙulla yarjejeniya da gwamnatin jihar domin kawo cigaba mai ɗorewa.
Gwamnan ya ƙara da cewa, jihar itace ke jagorantar dukkanin jihohi ta fannin amfani makamashi na hasken rana (renewable solar energy) a turance wanda a cewar sa abin alfahari ne ga al’ummar Jihar Katsina.
Haka kuma, Gwamna Raɗɗa ya ce samun sauƙin matsalar tsaro ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu bayan ƙaurace wa na dogon lokaci, Dikko yace wannan ya ƙara ƙarfafa harkar noma da kuma jawo hankalin masu zuba hannun jari zuwa jihar.
Bugu da ƙari, Jihar Katsina na cikin jihohin da suke kan gaba a shirye-shiryen Bankin Duniya, musamman a fannoni irin su Ilimin ’ya’ya mata, ci gaban rayuwarsu, da sauran muhimman shirye-shiryen da ake aiwatarwa a ƙarƙashin tallafin Bankin Duniya( AGILE).
Shugaban kamfanonin kusan duk manyan ‘yan kasuwar jihar Katsina ne.
Sun kuwa haɗa da hamshaƙin ɗan kasuwa kuma shugaban MaxAir, Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal, Sanata Ibrahim Ida (Wazirin Katsina), Alhaji Abdulmutallib Funtua, da wasu kamfanoni kamar Cordros, Constrix, da sauran su waɗanda da dukkan su sun halarci taron.
Wata kafar sadarwa ta yi hira na musamman da Gwamna Dikko Raɗɗa kan ƙoƙarin da yayi na magance matsalar rashin tsaro da ƙarfafawa waɗannan kamfani kafin gwiwa na zuba jari a jihar.
Ya kuma yi bayani kan nasarori da ya sami kan tafiye-tafiye da yayi zuwa wasu ƙasashen waje da suka haɗa da yarjejeniyar da ƙasar Belarus kan taimakwa jihar kan tsaro da kuma ƙasar Faransa ita kuma samar da 1 Megawat na wutar lantarki da za ayi amfani da su a madatsar ruwa na Danja,”A jihar Michigan na ƙasar Amurka kuwa ta samar wa jihar Katsina da magunguna na kiwon lafiya kwantenoni da yawa.
