Talauci da rashin aikin yi ne ke hura wutar rashin tsaro a Arewa – Gwamna Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya bayyana cewa, talauci da rashin aikin yi su ne musabbabin rashin tsaro a Arewa.

Ya yi bayanin hakan ne a wata tattaunawa da ya yi a wajen taron zuba jari da haɓaka tattalin arziki (Katsina Economic and Investment Summit 2025) a jihar Katsina.

Gwamna yayi bayani gamsasshe ga mahalarta taron kan ƙoƙarin gwamnatinsa na kawo cigaba mai ɗorewa a jihar.
An cimma yarjeniyoyi da dama tsakanin jihar Katsina da wasu manyan kamfanoni daga ciki da wajen jihar da nufin inganta kasuwanci da tattalin arziki a jihar.

Manyan ‘yan kasuwa sun ayyana saka hannun jari na kimanin Naira N489bn a taron ƙarƙashin jagorancin Gwamna Raɗɗa, wanda ke nuna ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnan ya kawowa jihar.

Gwamnatin jihar ta siya hannun jarin kaso 20 (20%) a kamfanin Funtua Inland Dry Port.

Haka kuma jihar Katsina ta saka hannun jarin kaso 20 (20%) a kamfanin Funtua Brickworks.

Ta sa hannu kan yarjejeniya tsakaninta da kamfanin ABIL, Dar Al Halal don bunƙasa sarrafa nama da kuma madara ta dabbobi.

Duk a wajan taron, Katsina ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Torq da Goal Energy Investments don kafa wasu kamfanoni a jihar da ƙaddamar da yarjejeniya tsakanin kamfanin CONSTRIX da Katsina United Club.

Gwamnan ya bayyana cewa jihar ta samu nasarar jawo wannan ɗumbin alherin ne saboda wasu tsare-tsare da ta zo dasu.

Ya bayyana cewa an kafa tsarin tsaro na al’umma, wanda ya haɗa matasa sama da 2,500 da kuma kwamitocin tsaro a matakai daban-daban, don dawo da zaman lafiya a ƙauyuka da kuma farfaɗo da harkokin noma.

“Gwamnatin ta aiwatar da manyan gyare-gyare na gudanarwa irinsu ƙirƙirar asusun bai ɗaya (TSA), hukumar ICT ta jihar, da kuma tsarin SPIME da PSR don bibiyar harkokin gwamnati,”Inji Dikko Raɗɗa.

Harwala yau gwamnati ta inganta harkokin ƙasa da safiyo ta hanyar GIS (KATGIS), sannan an ƙaddamar da tsarin rijista na yanar gizo don inganta rajistar kasuwanci.

Gwamnan ya sanar da haɗin gwiwa da Bankin Duniya, UNDP, da wasu abokan tarayya na Amurka wajen bunƙasa gidaje, samar da kayan lafiya, da kayan inganta ilimi.

An kuma faɗaɗa shirin “Nigeria for Women” zuwa duk ƙananan hukumomi 34 na jihar tare da ƙarin kuɗi N4bn na gwamnatin jiha don inganta shirin da dai sauransu,”Inji Raɗɗa.

Gwamnan ya bayyana an fara aikin samar da tashar wutar lantarki (1 MW) a Danja don samar da wuta mai aiki da hasken rana. Har ila yau, jihar ta rattaɓa hannu kan yarjejeniya da Hukumar Tsaro ta Iyakokin Belarus don ƙara tabbatar da tsaro.

Malam Dikko Raɗɗa ya jaddada cewa duk waɗannan matakai ba wai don samun riba kawai ba ne, sai don gina masana’antu, samar da ayyuka, da inganta rayuwar jama’a, musamman matasa da mata.

Mahalarta taron sun haɗa da Wazirin Katsina, Sen Ibrahim Ida, Ministan Jinkai, Hon Tanko Sununu, wakilan gwamnonin Kaduna, Zamfara, Yobe, Kano da Yobe, hamshaƙan yan kasuwa, Alhaji Umar Mutallab da Alhaji Dahiru Mangal da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin Nijeriya.

By ukarofi