Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin madatsar ruwa a Faskari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan aikin madatsar ruwa da za a fara a garin Sabon Layi da ke ƙaramar hukumar Faskari ya biyo bayan fara samun zaman lafiya a yankin da su kai ta fama da ta’addanci.

Aikin, wanda shirin ACReSAL zata ɗauki nauyi, zai samar da ruwa ga dubban mutane dake yankunan tare da haɓaka tattalin arziki ga al’ummar yankin musamman bayan fara samun sauƙi daga iftila’i na rashin tsaro.

Da yake ƙaddamar da fara aikin,Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana aikin a matsayin hanyoyin da gwamnati ke bi na dawo da harkokin yau da kullum a yankunan da matsalar tsaro ya addaba a yankunan Katsina.

Dikko ya tabbatarwa da alummar yankunan da jihar Katsina cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kawo ire-iren waɗannan ayyuka don cigaban jihar Katsina.

A nashi jawabin, kwamishinan Muhalli, Alhaji Hamza Sule Faskari yayi godiya ga gwamna akan ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta tsaro da walwalar al’umma. Ya kuma bayyana shirin ma’aikatarsa na tabbatar da bin diddiƙin aikin har a kammalashi.

A jawabinsa, wakilin shugaban shirin ACReSAL, Yusha’u Elsunais yace aikin dam ɗin, da zai iya ɗaukar ruwa mai yawan 700,000 Cubic Meters za’a kammalashi ne cikin shekara ɗaya da rabi.

Shugaban kamfanin da zasuyi aikin, International Consolidated Contractors Offshore da Badawi Azour Trading and Contracting Company, yayi godiya ga gwamnan jihar Katsina tare da tabbatar masa cewa zasuyi aiki mai inganci kuma akan lokacin da aka gindaya.

By ukarofi