Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na 2026

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A jawabinsa bayan da ya sanya hannu a kasafin kuɗin ya bayyana cewa kaso 80 bisa ɗari na kasafin kudin zai tafi a wajen manyan ayyuka,sai kuma 18 bisa ɗari zai tafi wajen harkokin yau da kullum.

Ya ce wannan kaso shine karo na farko tun kirkiro da jihar Katsina da aka ware kaso na 18 bisa ɗari kan harkokin yau da kullum “tun lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’adua yana gwamnan Katsina.

Dikko Raɗɗa ya yabawa Yan majalisar dokokin jihar kan yadda suka sadaukar da lokacin wajen tabbatar da komai ya tafi daidai kan kasafin kuɗin.

“Kun hana kanku barci wajen kiran shugabanin ma’aikatu domin su yi bayani kan kasafin kuɗin wanda hakan abin a yaba ne,”Inji Dikko.

Gwamnan ya yaba da irin kyawawan dangantaka da ke tsakanin ɓangaran zartarwa, majalisa da ɓangaran shari’a.

Ya bayyana kasafin kuɗi na 2026 a matsayin na al’umma domin a cewar sa sai da masu ruwa da tsaki na mazaɓu 361 suka gabatar da buƙatar al’ummar ga gwamnati kafin ta tsara Kasafin kuɗin.

A jawabinsa kafin miƙa kundin kasafin kuɗin,kakakin majalisar dokokin jihar Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya bayyana cewar sai da majalisar ta bibiya ga kasafin kudin sahu da ƙafa kafin ta amince.

Majalisar ta lura da tsarin kasafin kuɗin ya daidai da buƙatar al’ummar jihar shi yasa majalisar ba ta rage ko ƙara ko kobo a Kasafin kuɗin ga gwamna ya gabatar na Naira biliyan 899.86.

By ukarofi