Da Ɗumi-Ɗumi: An kama shugaban ƙasa bayan hamɓarar da gwamnatin dimukraɗiyyar Guinea-Bissau

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Guinea-Bissau sun bayyana cewa sojoji sun yi nasarar kifar da gwamnatin dimukraɗiyyar ƙasar tare da kama Shugaba Umaro Sissoco Embalo.

A cewar jaridar TheAfricaReport, an kama Embalo ne a yau Laraba da misalin ƙarfe 1 na rana a lokacin da yake ofiahinsa a Fadar Shugaban Ƙasa.

Haka kuma, an kama Babban Hafsan Tsaron ƙasar, Janar Biaguê Na Ntan; mataimakin shugaban ma’aikata, Janar Mamadou Touré; da kuma ministan harkokin cikin gida, Botché Candé.

A cewar Shugaban ƙasar mai barin gado, babu wani ƙarfin soja da aka nuna masa a yayin juyin mulkin, wanda aka ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin shugaban sojoji.

Hakan na zuwa ne yayin da rikicin siyasa ya yi ƙamari tsakanin Shugaba Embaló da babban abokin hamayyarsa, Fernando Dias bayan zaɓen da suka gwabza.

A makon da ya gabata ne, ranar Lahadi aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar, inda dukkanin ƴan takarar biyu suke ikirarin yin nasara. Shugaba Embalo ya ce ya yi nasara da kaso 65.

By Babaji