
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) na Arewa da Abuja, Reberen John Hayab ya ce wani mahaifi da aka yi garkuwa da ƴaƴansa uku daga cikin waɗanda ƴan bindiga suka sace a makarantar St. Mary a Jihar Neja, ya rasu bisa takaicin al’amarin.
Da yake magana yayin hira da gidan talabijin na Arise News a jiya Talata, Hayab ya ce wani mai suna Mista Anthony shi ne wanda ya rasa ran nasa.
Ya bayyana cewa, mutumin ya haɗiyi zuciya ne a lokacin da ya ji labarin cewa ƴaƴan nasa uku suna daga cikin waɗanda aka sace a makarantar. Al’amarin ya ƙaru akan waɗanda suka faru a jihohin Kebbi, Kwara da Neja.
Hayab ya bayyana al’amarin a matsayin abinda ya shafi iyalai da dama duba da cewa suna fargabar fitowa su yi magana a bainar jama’a koda an nemi ji ta bakinsu.
A lokacin da ya kai ziyara ga wasu jami’an coci a Kontagora, Reberen Hayab ya bayyana irin ƙuncin da iyalai suke ciki game da halin da ƴaƴansu suke ciki da kuma inda suke.
Haka kuma ya soki rashin isassun jami’an tsaro a yankunan da al’amarin ya shafa wanda hakan ke haddasa hare-hare da garkuwa da mutane acikin al’umma.
