Marasa ƙaunar talaka ne ke sukar auren zawarawa da kai ɗaliban Kano waje karatu – Dabinai

Manhaja logo
Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Alhaji Zubairu Suleman Dabinai, Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Ɗan Tunku Traders Association, ya bayyana cewa su dai suna goyon bayan auren zawarawa wanda ake kira da auren ‘yan gata da kuma kai ɗalibai ‘ya’yan talakawa marasa ƙarfi karatu ƙasashen waje duk da suna da cikakkiyar masaniyar cewa wasu masu ƙarfi da madafan iko marasa ƙaunar talaka ba sa goyon bayan wannan al’amari na alkairi a Musulunce da al’adance da zamantakewa ta mutanen kirki masu ƙaunar talaka da ‘ya’yansa na a ga an cigaba an yi ilimi mai zurfi kuma an taimakawa marasa ƙarfi ta kowacce fuska, “amma duk wani wanda ke da ƙarfin aurar da ‘yay’ansa maza ko mata ko kuma yake da qarfin da zai kai ‘ya’yansa waje ko wacce ƙasa karatu to duk marasa ƙaunar talaka basa ƙaunar wannan lamari na gwamnatin Kano ƙarƙashin shugabancin Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf,” kamar dai yadda shugaban wannan ƙungiya ya bayyana a wannan lokaci.

Har ila yau ya ce aure a kowane addini da ko wacce al’ada abu ne mai kyau amma mu Musulmi aure abu ne muhimmanci kuma jigo a samar da tsarkarkiyar al’umma kuma bai zama baƙon abu ba tun shekarun baya motanen kirki na taimakawa wajan aurar da ‘yan uwansu da maƙuta da sauran talakawa kuma har tashin duniya mutanen kirki ba za su daina abun kirki ba kamar yadda akasin mutanen kirki za su cigaba da rashin kirki.

“Saboda haka gwamnati da saura al’umma a dage wajen tallafawa al’umma da gina ƙasa musamam a wannan hali da al’umma dake cikin matsi na rashin abinci da sauran matsaloli na rayuwa masu yawa.”

A ƙarshe Alhaji Zubairu Sulaiman Dabinai, ya jadada shawara wajen ganin gwamnati da sauran al’uma na a taimakawa al’uma kan wannan matsi da ake ciki na rayuwa kuma a dage da adua wajen ganin Allah, ya tsayawa wanda yake taimakon bayinsa ya kuma karya masu son ganin abu mara daɗi ya aukawa kano ko Nijeriya, don haka akwai buqatar addu’ar ta musammam ta zaman lafiya a Kano da Nijeriya baki faya.

By Editor